✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Akwai bambancin Kannywood a da, da a yanzu—Mansurah Isah

Zagi da kirana sunaye marasa kyau babu wanda ba a yi min ba a kafafen sadarwa.

Aminiya ta zanta da tsohuwar jaruma a masana’antar Kannywood, wadda yanzu take shirya fina-finai kuma take shugabantar gidauniyar taimakon al’umma, inda ta bayyana nasarorin da ta samu da batun rabuwar aurenta da Sani Danja da sauransu.

Fim din ki na Fanan ya samu karbuwa sosai a sinima. Mene ne sirrin?

Alhamdullillah, ba abin da zan iya cewa sai dai in ce na gode wa Allah. Domin hanyoyin da na bi ne na tallata fim din da addu’a da rokon Allah da jajircewa, don duk lokacin da na sa wakar Fanan din a kafofin sadarwa, ina ganin bayanan da masoya ke yi suna cewa ‘mu dai kin addabe mu’. Amma na san abin da nake yi, ina yi ne don fim dina ya samu karbuwa, kuma ina so in ajiye tarihi, kuma na yi. Saboda haka, ba ni da abin da zan ce sai dai in ce Alhamdullillah.

Me ya sa kika sa wa fim din suna Fanan?

Duk lokacin da zan yi fim, nakan so in sami dan gajeren suna, saboda idan wani yana son tuna sunan fim din ba sai ya yi dogon tunani ba. Sannan kuma ina duba halin jarumar cikin fim din da yanayinta. Me za ta yi ko kuma wacce irin mace ce a cikin fim din. Sai kuma in duba kamilalla ce? Sai in tafi in nemi suna na kamilalla. In na ga masifaffiyace, sai in nemi suna irin na wadanda ba sa jin magana. Yadda na samo sunan Akeela da Fanan ke nan.

Har yanzu dai a kan fim din Fanan. Me za ki ce ganin yadda ya dauki hankalin mutane?

Kamar yadda na ce miki, gaskiya ba na cikin hurumin da zan iya cewa fim din Fanan kaza ne, yin Allah ne. Saboda ni ma da kaina ban yi tsammanin fim din zai kai haka ba.

Amma kuma ya zo ya wuce tunanina da lissafina, in aka ce in ce wani abu, kamar dama can ina tsammani ke nan. Abin da na yi kawai shi ne, na yi kokarin tallata fim dina, ya kuma samu karbuwa, don mutane sun ji dadinsa. Kuma na ga jawabai da dama inda mutane ke cewa sun ji dadi, ya yi musu kyau.

Ni ma da kaina na ji dadi don fim din ya yi kyau. Da farko ina ta jin tsoro, ina ta tunani ko mutane za su karbi fim din. Ana gobe za a saki fim din ko barci ban yi ba. Haka na zauna har gari ya waye, ina ta tunanin ko zai samu karbuwa ko ba zai samu ba.

An gan ki da tsohon mijinki Sani Danja a wajen kallon fim din, kuna ta annashuwa, ko akwai wani abu ne a kasa?

Ni ban ga abin mamaki ba, uban ’ya’ya na ne, abokina ne kuma abokin sana’ata ne, ban ga wani abin mamaki ba, ko bajinta ba. Duniya ta riga ta canja, da da yanzu ba daya ba ne.

Da ne idan mace da namiji ba sa tare, sai a ce hanyar da yabi ba zan bi ba, ko hanyar da ta bi ba zai bi ba, a wane dalili? Abin da ya hada ya hada, ba wanda zai iya raba wannan abin. Saboda da haka, ban ga wani abin mamaki ba, ai mutane ba su ce shi ke nan har abada ba.

Game da gidauniyarki ta taimaka wa marasa karfi. Yaya kike samun kudi?

Game da gidauniyata mai suna ‘Today’s Foundation’, na farko ina aiki, wani lokaci idan na yi aiki, kudaden da aka ba ni na aikin da na yi, nakan yi amfani da su wajen taimaka wa mutane.

Sannan kuma ni ma mai iyali ce, ina da ’ya’ya, ina da iyaye da ’yan uwa, ina da abokan arziki da suke neman taimako a wajena. Tunda har zan iya fitowa in taimaka wa wani a waje, dole ne in taimaka musu suma.

To idan na ga ba ni da kudi, aljihuna ya fara yi kasa, ba ni da kudin da zan taimaka wa mabukatan, sai in nemi tallafi ta kafar sada zumunta ta zamani, sai in saka bayanin cewa wannan bawan Allahn yana neman taimako, don Allah a taimaka masa ko mata.

Ko kuma idan za mu yi wani shiri kuma zai bukacikudi da yawa, shi ma sai in fito yanar gizo, in ce muna da kaza da za mu yi, duk wanda ya yi niyya ya tallafa mana domin samun nasarar abin, to ya shigo.

Sai ku ga wasu masu dubu daya, dubu biyu, dubu goma, har da masu dubu hamsin, duk dai masu taro da sisi. Duk za su aiko a hada. In aka harhada kudin na tabbatar wannan aikin da kudin mutane a ciki, ina gama aikin nan zan sa shi a yanar gizo, don su tabbatar cewa an yi amfani da kudin yadda ya kamata.

A matsayinki ta tsohuwar jaruma, yaya za ki kwatanta Kannywood a zamaninku da yanzu?

Gaskiya Kannywood din da da yanzu ba daya ba ne. A Kannywood din da akwai wahala wani lokaci ma za ka yi fim har ka gama, ba ka san me kake yi ba don ba ka da labarin.

Sai ka zo wajen daukar fim sai a fada maka yanzu alhaji zai fito, zai dalla miki mari, sai ki yi haka, ki yi kuka, ki fadi, shi ke nan fa an gama fim. Shi ya sa ba a samun abin da ake so, saboda ba ka san me kake yi ba.

Sai ka zo ka ga an hada fim sai ka ce ni da an fada min ga labarin da na yi abin da ya fi haka, da ke nan. Kuma ba mu da kayan aiki, gaba daya in kika shiga YouTube yanzu, za ki kalli fim din da, ba za ki ga fuskokinmu ba.

Ni yanzu idan na shiga YouTube na kunnawa ’ya’ya na tsofaffin fim dina, dariya suke min, su ce Maman Iman wa ce ke? Maman Imam ke ce nan? A’a Maman Iman ke ce wancan, ba su gane fuskar ba. (Dariya). Domin kayan aiki a lokacin mu ba a ci gaba ba. Yanzu kuwa akwai kayan aiki irin su Mac 3, Mac 4, da dai sauransu. Yanzu akwai kayan aiki an ci gaba.

Kai har bikin za a fara fim ake yi, a tara ’yan fim a ci abinci, a ba su labarin fim din, a ba kowa rawar da zai taka ya tafi gida ya je ya karanta don ya san abin da zai yi a fim din. Kin ga ba za ki iya hada da da yanzuba. Amma a da mun fi kokari, kuma mun fi mayar da hankali a kan fim din.

Saboda mu ’yan fim din da mun fi sha’awar fim, muna son fim. Muna yin sa ne da cikin zuciyarmu. Amma yanzu mutane sun mayar da shi bari in yi don na yi suna, in na yi suna kawai in tafiya ta.

Yaya alakarki da sauran tsofaffin jaruman Kannywood?

Ina da kyakkyawar alaka da kowa, duk wanda ya san ni, ya san ni da murmushi kodayaushe, ya san ni da kyautatawa, ya san ni da girmama na gaba da ni, ya san ni da zaman lafiya da kowa. Duk wata ko wani a masana’antarmu, ba wanda ba na magana da shi.

A gidauniyar kina shirya fina-finai, ko me ya sa?

Ba gidauniya ta ba, kamfanina, ina da gidauniya mai suna ‘Today’s Life Foundation’ mai zaman kanta, wadda ke tallafa wa marasa karfi da al’umma, ‘Today’s Life Nigeria Limited’ shi ne kafanina da muke aikin gine-gine da kwalliyar gidaje. Ina kuma harkar fim, ina saye da sayarwa da sauransu, kuma ina biyan harajina duk wata (Dariya).

’Yayanki sun fara fitowa a fim, kina so su zama jarumai ne kamar ke da mahaifinsu?

A’a, kin san fim yana da wani abu guda daya, yana da shiga rai, daga ka hadu da ’yan fim sau daya, ka kalli fim ko aka yi fim a gabanka sau daya, ko sau biyu, sai ka ji sha’awarsa.

Ni ma abin da ya faru da ni ke nan, amma idan wurin cin abincinsu ne, ba za mu iya hana su ba.

A yanzu dai fim dinmu suke yi, kuma ba don kudi suke yi ba, sha’awa ce kawai, amma ba burinsu ba ne. Amma idan sun girma sun ce ga abin da suke so, idan fim ne, ba za mu hana su ba, rayuwarsu ce.

Wanne kalubale kike fuskanta da kika rabu da mijinki?

Hmm na dade ina so a yi min wannan tambayar, amma na yi ta nazari a kan irin amsar da zan bayar da ba za ta zame min matsala da tashin hankali Arewa ba, da ba za ta taba rayuwar ’ya’yana da rayuwata da rayuwar duk mutumin da yake alaka da mutunci da ni ba.

Amma in aka ce kalubalen da macen da ta fito daga gidan miji take fuskanta (ta dan tsaya ta girgiza kai ta yi murmushi), kawai ba abin da zan iya cewa sai dai na ce wa duk matan da ba su da aure a yanzu da suke da shi a da suka fito daga gidan miji, ina so in ce masu, su ci gaba da hakuri, domin Allah Ya san wane hali suka shiga, Allah Ya san dalilin da ya sa suka fito daga gidan aurensu, Ya kuma san wanne irin yanayi suka samu kansu a ciki.

Akwai abubuwa da yawa, yau in mace na fuskantar kunci a gidan aure, sai ta fadi ta mutu, sai ka ji ana cewa, me ya sa ba ta fito ba? Sai ta fito, don ba ta so ta mutu, kuma ba ta so ’ya’yanta su yi asararta a matsayin ta na uwa.

Tana fitowa, sai kananan yara a unguwa, wadanda ba su san me ake kira aure ba a cikin gari wadanda iyayensu ba su koya musu tarbiya ba, sai su fara ce-ce-ku-cen cewa ai bazawara ce, ai ta fito karuwanci ne, ai da ma zaman auren ne ba ta so da sauransu. Akwai macen da take zaman aure, take jin dadin aure, take samun bukatar aure, take cikin nutsuwa a cikin aure, take samun duk wani abu kawai sai ta ji tana so ta fito waje?

Babu macen a duniya, wallahi babu macen a duniya. Zagi da kirana sunaye marasa kyau babu wanda ba a yi min ba a kafafen sadarwa. Abin da idona ya gani a rayuwa ba zan iya roka wa makiyana su ba balantana ’ya’yansu ko ’yan uwansu ba.