Shugaban Nana Akufo-Ado na kasar Ghana ya lashe zaben shugaban kasar wanda zai ba shi damar yin wa’adi na biyu.
Hukumar zaben kasar ta sanar cewa Shugaba Akufo-Ado na jam’iyar NPP ya samu damar yin tazarce ne bayan da ya samu kuri’a 6,730,413, kashi 51.59 cikin 100 na kuri’un da aka jefa.
- Budurwa ta banka wa masoyinta wuta don ya ki aurenta
- ‘Yadda auren dana zai kasance da matar sa Ba’amurikiya’
Shugaban mai ci ya kayar da babban abokin hamayyarsa daga jam’iyyar NDC, tsohon Shugaban Kasar, John Dramani Mahama, wanda ya samu kuri’a 6,214,889 (kashi 47.36% na kuri’un da aka jefa).
A ranar Litinin mutum miliyan 17 na fadin kasar Ghana suka fara jefa kuri’u a zaben wanda jam’iyyu 12 suka fafata a ciki.
Manyan ’yan takarar su ne Shugaba Akufo-Ado mai ci da ke neman tazarce, da gabacinsa, Mista Mahama wanda ke neman dawowa ya yi mulki a karo biyu.
Sauran abokan hamayyar tsofaffin shugabanin kasar sun hada da Mista Christian Kwabena Andrews na jam’iyyar GUP; Madam Brigitte Akosua Dzogbenuku ta jam’iyyar PPP; Madam Akua Donkor ta jam’iyyar GFP; da Nana Konadu Agyemang-Rawlings ta jam’iyyar NDP
Sauran sun hada da: Dokta Hassan Ayariga na jam’iyyar APC; Ivor Kobina Greenstreet na jam’iyyar CPP; Henry Herbert Lartey na jam’iyyar GCPP; da kuma Percival Kofi Akpaloo na jam’iyyar LPG.
Akwai kuma Mista Alfred Kwame Walker na jam’iyyar IC; da kuma David Asibi Ayindenaba Apasera na jam’iyyar PNC.