Gwamanan Jihar Osun Gboyega Oyetola ya taya takwaransa na Jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu murna bisa nasarar da ya samu a zbaen gwamnan da ya gudana ranar Asabar.
Oyetola wanda shi ne Shugaban Kwamitin Jmam’iyyar APC na kasa kan yakin neman zaben Akeredolu ya ce gwamnan ya cancanci zaben da jama’ar jihar suka yi masa.
“Wannan nasara alama ce ta hakikanin fata da burin jama’ar Ondo kuma a bayyane yake cewa nasarorin Gwamna Akeredolu ya samu a ayyukan da ya aiwatar a wa’adinsa na farko ne ya sa suka suka sake zaben shi.
“Ina da kwarin gwiwa zai dora a kan ayyukansa na samar wa jama’ar jihar romon dimokuradiyya da ya faro a wa’adinsa na farko”, inji sakon da kakakin Oyetola, Ismail Omipidan, ya fitar bayan INEC ta sanar da sakamakon zaben.
Sanarwar ta kuma taya Shugaba Muhammadu Buhari da sauran shugabanni da magoya bayan jam’iyyar APC murna bisa nasarar da aka samu a zaben.
A ranar Lahadi ne Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar cewa Akeredolu ya lashe zaben na ranar Asabar bayan samu kuri’a 292,830.
Babban abokin hamayarsa, Eyitayo Jegede na jami’ar PDP ya samu kuri’a 195,791 a matsayi na biyu.
Mataimakin Gwamnan, Agboola Ajayi, wanda suka dade da raba gari, da ya yi takara a karkashin jam’iyyar ZLP shi ne na uku da kuri’a 69,127.