Wani yaro mai shekara 11 a duniya ya gamu da ajalinsa yayin da ya fada rafi a unguwar Dafa da ke yankin Kwali a Abuja.
Wani mazaunin yankin mai suna Dogara ya ce lamarin ya faru da ne misalin karfe 2 na yammacin ranar Litinin.
– Akwai yuwuwar yawan ruwan sama ya hana jirage tashi – NIMET
– Na so a ce ’yata ta kammala karatu kafin ta auri dan Buhari – Sarkin Bichi
A cewarsa, yaron ya fada rafin ne yayin da yake kokarin tsallakawa a unguwar Dafa-Tunga-Gwomani.
Ya ce yaron ya bar gida ne da nufin zuwa gona don taya mahaifinsa aiki, yayin da lamarin ya faru.
“Har ya tsallaka rafin sai ya tuna cewar ya manta fartanyarsa, shi ne ya sake dawowa don ya dauka, a lokacin ne kuma ya nitse a ruwan,” a cewarsa.
Shugaban yankin Dafa, Alhaji Abdullah Kajiya, wanda ya tabbatar da rasuwar yaron, ya ce har ya zuwa lokacin da muka zanta da shi ba a ga gawar yaron ba.
Ya ce an gayyato masunta inda suka shiga neman gawar yaron tun a yammacin ranar Litinin, amma ba a kai ga dace ba tukuna.
“Mamakon ruwan da aka yi ranar Litinin na da yawa, wanda na dawo fada aka sanar da ni rasuwar wani yaro mai shekara 11 a duniya,” cewarsa.