✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Aisha ta bukaci Buhari ya kawo karshen garkuwa da ’ya’ya mata

Rashin tsaro da bullar annobar COVID-19 sun jefa mata cikin tasku

Uwar gidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta yi kira da a samar da cikakkiyar tsaro ga ’ya’ya mata a Najeriya ta yadda za su samu cikakken ilimi ba tare da tarnaki ba.

Aisha Buhari ta yi kiran ne a sakonta na zagayowar Ranar Mata ta Duniya ta 2021, inda ta bayyana damuwa kan yadda garkuwa da ’ya’ya mata ke kawo musu cikas wurin neman ilimi da kuma jefa iyalansu cikin tashin hankali.

“A matsayina na uwa, ina cike da bakin cikin wannan lamari da ya bari daliban da danginsu cikin jimami,” inji ta.

Ta cewa wannan ba karamar koma-baya ba ne ga nasarorin da aka samu wurin ilimantar da yara mata.

Da take jajanta wa iyalan yaran da ’yan bindiga ko kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su, Aisha Buhari ta roki gwamnati a dukkan matakai da ta tabbatar da kariya da aminci ga yara mata a duk inda suke.

Ta ce mata sun shiga matsi sakamakon bullar COVID-19 wanda hakan ya yi mummunan tasiri ga rayuwarsa ta fuskoki iri-iri.

“COVID-19 ta yi matukar tasiri a kan mata; ta hargitsa ilimi da sana’oi, ga rasa ayyukan yi; karuwar talauci; da kuma rigingimu a cikin gidaje.

“Mutane da yawa kuma sun sun mutu ko sun shiga wahala saboda rashin samun bayanai na asali game da cutar.”