✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A’isha: Marar hannuwa da ke gudanar da al’amura kamar kowa

Wata budurwa mai kimanin shekara 14 da ke Unguwar Nayinawa Tsamiyar Lilo a garin Damaturu fadar Jihar Yobe, wadda ba ta da hannuwa, tana gudanar…

Wata budurwa mai kimanin shekara 14 da ke Unguwar Nayinawa Tsamiyar Lilo a garin Damaturu fadar Jihar Yobe, wadda ba ta da hannuwa, tana gudanar da kusan dukkan ayyukan gida ta amfani da kafafunta.

A’isha Muhammad Maji, tana aji hudu ne a makarantar firamaren da ke Unguwar Nayinawa a Damaturu.

Duk da cewa abu ne da ya zamo ruwan dare a ga mai nakasa yana bara domin samun abinci, to amma al’amarin A’isha ya sha bamban da na sauran wadansu nakasassu, domin iyayenta sun tsaya mata don ganin ta yi karatu, duk da rashin kudi da suke fama da shi.

Yayin da wakilinmu ya ziyarci gidan su A’isha a Damaturu a Larabar makon jiya, ya tarar da ita tana amfani da kafafunta wajen dauko littafi daga jakarta ta makaranta, inda ta yi amfani da kafa daya domin bude jakar kuma ta yi amfani da daya kafar ta dauko littafin.

Daga nan ne kuma ta dauki biro da kafarta ta rubuta jimloli uku. Tana amfani ne da tsakanin babban yatsarta ta kafa da sauran ’yan yatsun domin gudanar da ayyukan da take son aiwatarwa.

Aminiya ta gane wa idonta yadda A’isha ke iya rubutu da Ingilishi da Larabci, ta yadda duk wani wanda ya iya karatu zai iya karantawa kuma ya fahimta.

“Duk da cewa ina da nakasa ba na samun tsangwama daga abokan karatuna a makaranta. Muna zama tare mu yi wasa, mu ci abinci tare. Iyayena suna taimaka min sosai saboda tunda na taso a haka na samu kaina, ba ni da hannuwa.

“Na yi farin ciki sosai da iyayena suka sanya ni a makaranta, domin in samu ilimi; maimakon su tura ni bara. Mahaifiyata tana koya min abubuwa da yawa. Duk da cewa ba ni da hannuwa, amma na koyi yin abubuwa da yawa da kaina,” inji ta.

Ta kara da cewa: “Ina shan wahala wajen ganin na kwaikwayi abin da iyayena da malamaina da abokaina suke yi saboda na ga suna yin abubuwansu cikin sauri da hannuwansu, amma cikin ikon Allah ina iya bakin kokarina kuma komai yana zuwa min cikin sauki.”

Da take ba da labarin yadda rayuwar ’yar tata mai shekara 14 ta kasance, mahaifiyar A’isha mai suna Malama Rabi ta ce lokacin da ta haife ta ba ta da wata nakasa a jikinta. Tana da hannuwanta biyu kamar kowane dan Adam mai cikakkiyar lafiya.

Rabi ta ce wannan mummunan al’amari ya faru ne lokacin da wata mota da ta zo wucewa ta buge A’isha, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa hannuwanta biyu tun tana ’yar shekara biyu a duniya.

“Lamarin ya tayar da hankalinmu gaba daya amma mun gode wa Allah da Ya sa ta rayu. Mahaifinta yana iya bakin kokarinsa don ganin ya ba ta duk wata kulawa da kowace ’ya take so,” inji Rabi.

Ta ce bayan rubutu da yarinyar ke iya yi, A’isha tana yin ayyukan gida kamar shara, wanke-wanke da kuma wanki, sannan tana kula da kannenta a gida duk ta hanyar amfani da kafafunta.

Rabi ta yi kira ga gwamnati da kungiyoyin taimako masu zaman kansu su taimaka wa A’isha don ganin ta yi karatu, sannan a samar mata kayayyakin aiki da jari da za ta iya yin sana’a a gida.

“Mun gode wa Allah saboda mun ci gaba da daukar dawainiyarta tsawon wadannan shekaru. Amma ina tsoron ko karatunta zai dore nan gaba? Ina tunanin gaba saboda makarantar da take zuwa yanzu ba ta da nisa da gida, sannan akwai karamar sakandare a kusa, za mu iya sa ta idan ta gama firamare. Amma damuwar ita ce, babu babbar sakandare a kusa ta gwamnati wacce za mu iya kai ta, ga shi kuma ba za mu iya biya mata makarantar kudi ba,” inji mahaifiyar A’isha.