Uwargidan Shugaban Kasa, Hajiya Aisha Buhari ta raba wa masu karamin karfi a sassa daban-daban na Arewacin Najeriya kayan sa wa na gwanjo da yawansu ya kai dila 350.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa Aisha ya raba tallafin ne ta hannun gidauniyarta mai suna ‘Future Assured’, ga sauran kungiyoyi masu zaman kansu a jihohin Kano da Katsina da Adamawa da Zamfara da kuma Kaduna.
- Falasdinawa za su maka Isra’ila gaban kotun duniya
- ECOWAS ta dakatar da Burkina Faso saboda juyin mulkin sojoji
Rahotanni sun ce daga bisani su kuma kungiyoyin sun raba kayan ga mabukata, yawancinsu masu karamin karfi.
Wani jagoran daya daga cikin kungiyoyin a Jihar Kano, Sani Lawan ya ce jiharsu ce ta samu kaso mafi tsoka na tallafin kayan.
Ya ce kowacce daya daga cikin kungiyoyin da aka zaba an ba ta dilar gwanjon guda hudu ne, inda ya ce akasarin dilolin sun kunshi kayan sanyi ne domin kare yara daga hunturu.
Sai dai baya ga kungiyoyin masu zaman kansu, Sani Lawan ya ce an kuma raba wasu daga cikin kayayyakin zuwa gidajen marayu da asibitin masu tabin hankali da ke Jihar.