✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ainihin abin da ya faru da ɗan wasan Nijeriya Taiwo Awoniyi

Yana daga cikin tawagar Nijeriya da ta yi nasara kan Libya a wasan neman gurbin gasar Kofin nahiyar Afirka ta 2025.

An yi wa ɗan wasan gaba na ƙungiyar Nottingham Forest, Taiwo Awoniyi allurar barci mai nauyi domin taimaka masa murmurwa daga tiyatar da aka yi masa.

Bayanai sun tabbatar cewa an garzaya da ɗan wasan ɗan asalin Nijeriya asibiti ne domin yi masa tiyata a ranar Litinin, bayan ya samu mummunan rauni a cikinsa a wasan da suka tashi canjaras, 2-2 da Leicester a Gasar Premier ta Ingila.

Alamu sun nuna cewa rayuwar ɗan wasan mai shekara 27 ba ta cikin haɗari, kuma allurar barcin da aka yi masa za ta taimaka ne wajen tsagaita ayyukan zuciya da jikinsa wanda hakan zai taimaka wajen hanzarta samun sauƙi.

Awoniyi ya yi karo ne da ƙarfen raga sa’ilin da yake ƙoƙarin cin ƙwallo mintuna kaɗan gabanin tashi daga karawar tasu da Leicester.

Likitoci sun kwashe tsawon mintuna suna kula da shi kafin barin sa ya ci gaba da wasa, duk da raɗaɗin da yake ji, kamar yadda aka gani baro-baro, kasancewar a lokacin Forest ta ƙarar da yawan ’yan wasa da za ta iya canzawa.

A ranar Litinin aka kara tabbatar da munin raunin da ya samu bayan likitocin ƙungiyarsa sun kara duba shi, aka garzaya da shi asibiti domin yi masa tiyata.

Amma ranar Talata, Nottingham Forest ta fitar da sanarwa cewa “Awoniyi na samun sauki”.

A yayin wasan nasu an ga yadda aka samu wata ’yar rashin jituwa tsakanin mamallakin ƙungiyar Evangelos Marinakis da mai horas da ita Nuno Espirito Santo a cikin filin wasa jim kaɗan bayan kammala wasan a ranar Lahadi.

Bayan sukar abin da mamallakin ƙungiyar ya yi, Forest ta ce lamarin ya faru ne kasancewar Marinaki bai ji daɗin yadda Awoniyi ya ci gaba da wasa ba duk kuwa da raunin da ya samu.

Sanarwar ƙungiyar ta ce “Evangelo Marinakis bai ɗauki Nottingham a matsayin ƙungiyar ƙwallon ƙafa kawai ba, ya ɗauke ta a amatsayin wani ɓangare na iyalinsa — kuma yana ƙoƙarin ganin kowa ya yi amanna da hakan.

“Shi ya sanya bai ji daɗin abin da ya faru ba a filin wasa na Leicester City a ranar Lahadi.

“Matakin da ya ɗauka ya kasance na nuna tsantsar kulawa da tallafa wa daya daga cikin waɗanda ya ɗauka a matsayin nasa.”

Wane ne Taiwo Awoniyi?

Awoniyi ɗan asalin Najeriya ne mai shekaru 27 da ke taka leda a ƙungiyar Nottingham Forest da ke Birtaniya.

Ya tafi ƙungiyar ne a watan Yunin 2022 daga ƙungiyar Union Berlin da ke Jamus, kuma ya fara wasan ƙwallon ƙafa ka’in da na’in ne a ƙungiyar Liverpool a shekara ta 2015 kafin ya tafi wasu ƙungiyoyi a Jamus da Holland da kuma Belgium a matsayin aro.

Ɗan wasan na gaba ya taka wa Nijeriya a gasanni daban-daban a matakai daban-daban kafin buga wa ƙasar a babbar ƙungiyarta ta Super Eagles.

Yana daga cikin tawagar Nijeriya da ta yi nasara kan Libya a wasan neman gurbin gasar Kofin nahiyar Afirka ta 2025. Dan wasan na da aure da ɗa ɗaya.