✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aikin jarida zan koma idan na sauka daga mulki – Gwamnan Binuwai

Ya kuma ce ya yafe wa Buhari duk abubuwan da ya yi masa

Gwamnan Jihar Binuwai mai barin gado, Samuel Ortom, ya ce zai iya komawa dan jarida mai zaman kansa bayan ya bar mulki ranar Litinin mai zuwa.

Ortom, wanda ke wa’adinsa na biyu na Gwamnan dai ya fadi zaben Sanatan da ya tsaya don waliktar mazabar Arewa maso Yammacin Jihar a Majalisar Dattawa.

Da yake jawabi game da shirye-shiryensa bayan ya sauka daga mulki a wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Arise ranar Laraba, Ortom ya kuma zargi Fadar Shugaban Kasa da kashe makudan kudade wajen ganin bai yi nasara ba a zaben.

Ya ce, “Na san nawa aka ba Jihar Binuwai daga Fadar Shugaban Kasa domin tabbatar da na fadi zabe. Amma na rungumi kaddara, kuma na sha alwashin taimaka wa duk wanda ya zo a bayana, muddin ya nemi taimakona.

“Amma idan bai nemi taimakona ba, zan koma gonata. Zan koma na rungumi kasuwancina, zan ma iya komawa na zama dan jarida mai zaman kansa,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma yi zargin cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ciyar da Najeriya baya, amma ya ce ya yafe wa Buharin duk abin da ya yi masa, kamar yadda lttafin Baibul ya karantar.

Sai dai ya yi fatan cewa al’amura za su inganta a gwamnatin sabon Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu.

A baya dai Ortom ya sha zargin gwamnatin Buhari da rura wutar rikice-rikicen da suka jawo kashe-kashe a Jiharsa.