✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Aikin Hajji: Maniyyatan Kaduna 2 sun rasu kafin tafiya Saudiyya

Dukkan maniyyatan dai ’yan Karamar Hukumar Igabi ne

Maniyyata Aikin Hajji biyu daga Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna sun riga mu gidan gaskiya gabanin tashinsu zuwa kasar Saudiyya.

Mutanen da suka rasu su ne Yakubu Abdulsamad da Haruna, sun rasu ne a ranakun Lahadi da Litinin.

Jami’in alhazai na Karamar Hukumar, Aminu Surajo, wanda ya tabbatar da rasuwar ya kuma ce tuni aka yi jana’izarsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Rahotanni sun nuna cewa an tsara mamatan biyu za su kasance cikin rukunin farko na maniyyatan da aka tsara tashinsu zuwa kasar mai tsarki.

Akalla maniyyata 2,491 ne ake sa ran za su sauke farali daga Jihar Kaduna a bana.

A wani labarin kuma, mai rikon mukamin Gwamnan Jihar, Dokta Hadiza Balarabe, ta roki maniyyatan Jihar da su kasance jakadun Jihar da ma na Najeriya na gari a Saudiyyar.

Da take jawabi ga maniyyatan yayin jawabin bankwana kafin tashin su a Kaduna ranar Talata, Dokta Hadiza ta kuma roke su da su yi wa kasa addu’a kan halin da take ciki.