✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ahmed Musa zai koma kungiyar Leicester City

dan wasan kwallon kafa na Najeriya, Ahmed Musa zai koma kungiyar  kwallon kafa ta Leicester City da ke kasar Ingila daga kungiyar CSKA Moscow a…

dan wasan kwallon kafa na Najeriya, Ahmed Musa zai koma kungiyar  kwallon kafa ta Leicester City da ke kasar Ingila daga kungiyar CSKA Moscow a kasar Rasha.
dan wasan mai shekara 23 ya buga wa kungiyar CSKA Moscow wasa sau 168 inda ya zura kwallaye 54 tun lokacin da ya je kungiyar daga Kano Pillars ta Najeriya.
Ana sa ran Ahmed Musa ya taimaka wa kungiyar ta Leicester City a gasar cin Kofin Zakarun Turai da kuma rukunin firimiya na Ingila.
Ejan din dan wasan, Tony Harris ya shaida wa BBc cewa an riga an gama komai a game da komawar Musa, kuma ya ce Musa zai je kasar Ingila domin a gwada lafiyarsa.
Haka mai horar da ’yan wasan CSKA Moscow, Leonid Slutsky ya shaida wa manema labarai cewa Ahmed Musa zai bar kungiyar. Ya ce, “Idan kuka lura da yadda ake buga kwallo a kasar Ingila, za ku san cewa lallai Ahmed Musa zai dace da yanayin wasannin kasar.”