Shahararren dan kwallon Super Eagles na Najeriya Ahmed Musa ne aka zaba a matsayin Gwarzon Dan Kwallon kafa a Najeriya na 2018 da kafar watsa labaran wasanni ta Legit.ng ta shirya.
Kafar watsa labaran wasannin ta shirya gasar ce don zakulo ’yan wasan Najeriya maza da mata da suka yi fice a wasanni daban-daban a 2018 da suka hada da kwallon kafa na maza da na mata da wasan tebur tenis da guje-guje da tsalle-tsalle da sauransu.
A yayin gasar, an ba masu sha’awar wasanni ne damar kada kuri’unsu don zakulo wadanda suka fi cancantar lashe gasar.
Ahmed Musa ne ya fi yawan samun kuri’a a bangaren kwallon kafa na maza a Najeriya. Ya samu nasarar ce bayan ya zura kwallaye biyu a ragar Iceland a gasar cin Kofin Duniya a Rasha da yadda ya taimaki Super Eagles hayewa gasar cin Kofin Afirka da za a yi a bana da kuma yadda ya canja sheka daga kulob din Leicester City na Ingila ya koma kulob din Al-Nassr na Saudiyya.
A bangaren mata kuwa Azizat Oshola ce ta zama zakara a 2018 bayan ta taimaki kulobi din mata na Najeriya Super Falcons lashe Kofin Afirka karo na 9. Sannan a wasan tenis kuma an zabi Aruna Kuadri bayan ya zama na 26 a duniya. Haka kuma an zabi ’yan wasa daban-daban a sauran bangarorin wasanni.