Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa, ya ba da tallafin kudi na naira miliyan 100 ga zawarawa 5,000 da sauran marasa galihu a Jihar Filato.
Daya daga cikin masu yada wa fitaccen dan kwallom labarai, Mr Williams Gyang ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Jos, babban birnin jihar.
- Yadda aka damfari masu neman gidan haya Naira miliyan 60 a Legas
- Mutum shida sun mutu a hadarin mota a Jigawa
Gyang ya ce tallafin wani bangare ne a kokarin da Musa ke yi wajen rage wa marasa galihu radadin tsadar rayuwar da suke fuskanta.
Ya ce, an tattaro wadanda suka samu tallafin ne daga sassan jihar ba tare da la’akari da bambanci addini, ko kabilanci, ko makamancin haka ba.
”Matsalar tsadar rayuwar da jama’a ke fuskanta ta girmama, wannan ita ce gudunmawar da zan iya bayarwa don nuna kauna da kulawa ga zawarawa da marasa galihun da ke cikin al’umma.
“Don haka ina kira ga daidaikun mutane kowa ya taimaka wa marasa galihu a cikin al’umma gwargwadon hali,” inji Musa.
Wata mai suna Maryam Abdullahi, daya daga cikin wadanda suka ci moriyar tallafin, ta nuna godiyarta ga gwarzon dan kwallon bisa tallafin da ya ba su.
“Da kyar muke iya ciyar da iyalanmu saboda tsadar rayuwa, kudin da aka ba mu zai taimaka wajen rage radadin rayuwar da muke fama da shi,” inji Maryam.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, wannan ba shi ne farau ba da Musa ke tallafa wa marasa galihu da dukiyarsa.