Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya roki gwamnatin Saudiyya ta taimaka wajen dawo da ’yan Najeriya sama da 10,000 da ke tsare a Saudiyya.
Lawan ya yi rokon ne a yayin da Jakadan Saudiyya a Najeriya, Faisal Eebraheem Alghamdi, ya ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja.
Ya ce, “Muna sane cewa wasu daga cikin mahajjatanmu a baya suna da matsala a Saudiyya, dubbansu kuma suna tsare.
“A matsayinmu na kasa mun dauki matakan tabbatar da ilmantarwa da fadakar da ’yan kasa, musamman alhazai, cewa idan sun isa can, su yi ibadunsu sannan su dawo Najeriya,” inji shi.
Yayin jaddada rawar da Majalisar ke takawa wajen tabbatar da bin ka’idoji huldodin da Gwamnatin Najeriya ta shiga, Lawan ya bayyana cewa ana ci gaba da kokarin kwashe ’yan kasar da ke Saudiyya.
Ya ce, “Majalisar a koyaushe tana sane da tabbatar da cewa gwamnati na taka rawarta a ma’amalolin da gwamnatinmu ta yanke shawarar shiga.
“Saudiyya da Najeriya sun kulla kyakkyawar alaka na dogon lokaci, kuma alakar na kara bunkasa kowace shekara.
“Ina so na baku tabbacin cewa wannan bangaren na gwamnati zai yi aiki tare da ku a matsayin Ambasadan Saudiyya.
‘Za mu ci gaba da ilimantar da mahajjatan mu’
“Wannan zai rage yadda mutane ke makalewa a can kuma ba za su dawo ba.
“Ina tabbatar muku cewa za mu ci gaba da tallafa wa Hukumar Aikin Hajji ta kasa da na jihohi wajen ilmantar da mahajjatanmu.
“Kasarmu tana kuma yin iya kokarin ta don ganin mun kwashe ’yan kasarmu wadanda yanzu haka ke Saudiyya wadanda kuma muke ganin ya kamata su dawo gida. Ina son amfani da wannan damar don neman goyon bayan masarautar Saudiyya ta yi aiki tare da mu ta wannan hanyar don dawo da ’yan kasarmu.
“A yanzu haka, muna da ’yan Najeriya sama da dubu goma da ba su da rajista kuma ana tsare da su.
“Muradinmu ne mu tabbatar mun fitar da wadannan mutanen daga kasar sannan mun dawo dasu gida.
“Ina so na tabbatar muku cewa alakar da ke tsakanin wadannan manyan kasashen biyu – Saudiyya da Najeriya – za ta ci gaba ne kawai da samun ci gaba.”