✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Aguero zai yi ritaya daga tamaula saboda ciwon zuciya

Aguero zai yi ritaya daga tamaula saboda ciwon zuciya.

Rahotanni da ke fitowa daga nahiyyar Turai sun nuna cewa shahararren dan kwallon Argentina da yanzu haka yake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Sergio Kun Aguero, na shirin ritaya daga tamaula.

Fitaccen dan jarida a fannin wasanni, Fabrizio Romano ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafukansu na dandalin sada zumunta a yammacin ranar Asabar.

Romano ya ruwaito daga dan jaridar wasannin kwallon kafa a Sifaniya, Gerard Romero cewa Aguero zai ajiye kwallon ne sakamakon wasu matsaloli na rashin lafiya da suka danganci ciwon zuciya.

Aguero mai shekara 33 na shirin ritaya daga sanaar da ya shafe akalla shekaru 18 a matsayin kwararren dan wasa.

Ana sa rana cewa a taron manema labarai na mako mai zuwa da Barcelona za ta gudanar, za a sanar da halin da ake ciki game da makomar dan wasan dangane da ritayarsa daga tamaula.