✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Aguero zai yi ritaya daga buga kwallo ranar Laraba

Ciwon zuciya zai sa Aguero ya yi ritaya daga buga kwallo.

Dan wasan gaban Barcelona, Sergio Aguero ya bayyana aniyarsa ta jingine murza leda a sakamakon kamuwa da ciwon zuciya.

Dan wasan ya kamu da matsalar numshafi nw a wasan da Barcelona ta yi da Alaves a ranar 30 ga watan Oktoban 2021.

Da farko an bayyana cewa dan wasan zai shafe wata uku yana jinya, amma daga bisani yanayin nasa ya tsananta.

A ranar Laraba ake shirin yi wa Sergio Aguero bikin bankwana da buga kwallo, kamar yadda Emilio Perez de Rosas ya shaida wa gidan rediyon MARCA.

Rahotanni sun nuna cewa Barcelona ta shirya wa dan wasan bikin ban kwana don kara masa kwarin guiwa.

Barcelona ta dauki Aguero a karshen kakar wasanni, sai dai ciwon zuciya ba zai bari ta mori ci moriyarsa ba.

Dan wasan ya buga wasanni hudu ne kacal a gasar Laliga, wanda daga cikinsu ya zura kwallo daya a wasan hamayya na El Classico da kungiyarsa ta yi da Real Madrid.