✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Afirka ta Kudu ta kartaya batun amincewa da Keshi a matsayin kocinta

Shugaban Hukumar kula da kwallon kafar Afirka ta Kudu Mista Danny Jordan a ranar Litinin da ta gabata ne  ya karyata batun da ake yayatawa…

Shugaban Hukumar kula da kwallon kafar Afirka ta Kudu Mista Danny Jordan a ranar Litinin da ta gabata ne  ya karyata batun da ake yayatawa na cewa kocin Najeriya Stephen Keshi ya kulla yarjejeniyar kwantaragin shekara biyu don horar da kasar da zarar an kammala gasar cin kofin duniya da yanzu haka yake gudana a Brazil.
Kamar yadda mai magana da yawun Hukumar kwallon ta Afirka ta Kudu Mista Dominic Chimhabi ya shaidawa duniya, ya ce har yanzu kasar ba ta fitar da sunayen masu horarwar da za ta zabi daya daga ciki ba don haka bai san inda aka samo labarin Stephen Keshi ne aka zaba a matsayin wanda zai maye gurbin kocinsu na yanzu ba.
“Wannan labarin kanzon kurege ne kuma ba shi da tushe balle makama”, inji shi.
Tun lokacin da shugaban Hukumar FA ta kasar Mista Danny Jordan ya bayar da sanarwar kasar ba za ta sabunta kwantaragin kocinta Gordon Igesund aka fara rade-radin kocin da zai gaje shi. Shi dai shugaban ya bayar da tabbacin sai a watan Yuli watau bayan an kammala gasar cin kofin duniya ne kasar za ta bayar da sanarawar nada sabon koci.
Idan za a tuna, kocin Najeriya Stephen Keshi ya bayyana niyyarsa ta ajiye harkar horar da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da zarar an kammala gasar cin kofin duniya a Brazil al’amarin da ya sanya kasashe da dama ciki har da Afirka ta Kudu suke zawarcinsa.