✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Afirka na dandana kudarta a yakin Rasha da Ukraine — AU

Shugaban kungiyar, Moussa Faki Mahamat ne ya bayyana haka

Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU ta ce kasashen nahiyar Afirka sun zamo wani bangare da yakin Ukraine da Rasha ke yi;wa illa.

Shugaban kungiyar, Moussa Faki Mahamat ne ya bayyana haka ranar Laraba.

“Dagula yanayin siyasar duniya da tuni ya yi rauni sanadiyyar rikicin Ukraine din, ya haska raunin tsarin tattalin arzikin yankin na Afirka,” inji Moussa Faki.

Ya kuma ce rikicin da ake yi a halin yanzu na sake jefa duniya a mawuyacin halin karancin kayan amfanin gona, da hauhawar farashin kayan masarufi.

“Babbar hanyar da za a gane wannan rauni shi ne yadda aka samu karancin abinci biyo bayan matsalar yanayi da bangare lafiya aka samu, sakamakon annobar Kwarona, wanda ya karu sanadiyar yakin Ukraine.

A wani rahoto da kunfiyar ta AU ta fitar, ta yi gargadin cewa rikicin Ukaraine din zai ci gaba da durkusar da yankin wanda har yanzu ke fama da mashassharar annobar.

Ya ce dalilin hakan kuwa shi ne dogaro da kasashen yankin suka yi da kayan abincin da ake shigo da su daga kasashen na Ukraine da Rasha.

Kamar dai yadda rahotanni suka bayyana a shekara ta 2019, kasashen Afirka sun shigo da kayan abinci daga Rasha da suka kai na Dala biliyan hudu, kuma kashi 90 cikin 100 na kayan alkama ce.

Kazalika, yakin na Rashan ya janyo wa yankin hauhawar farashin takin zamani da kaso 21 cikin 100, wanda shi ma dai ya fi shafar kasashen Afirkan da suka dogara da noma.