A kasar Afghanistan, gwamnatin Taliban ta ce ta harbe wasu mutum hudu da ake zargi da garkuwa da mutane tare da rataye gawarwakinsu a tsakiyar birnin Herat don ya zama izina.
Matakin na zuwa ne ’yan kwanaki bayan wani jami’in gwamnatin kasar ya yi gargadin cewar za su dawo da tsauraran hukunce-hukunce a kasar.
- An kashe mutum biyu, an sace malamin tsangaya da wasu da dama a Zariya
- Tana kashe wa tantabaru 2 Naira miliyan 2 kan kayan kwalliya duk wata
An dai harbe mutanen ne yayin wata musayar wuta bayan sun yi garkuwa da wani dan kasuwa da dansa, kamar yadda wani jami’in gwamnati ya tabbatar.
Wani mazaunin yankin, Wazir Ahmed Seddiqi ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AP cewa an kawo mutanen ne tsakiyar gari inda aka rataye daya daga cikinsu, ragowar kuma aka wuce da su wasu wuraren sannan su ma aka rataye su.
Mataimakin Gwamnan Herat, Maulwai Shair ya ce an rataye su ne a bainar jama’a don ya zama izina.
Wasu hotuna da aka yada ta shafukan sada zumunta sun nuna yadda wata mota kirar A-kori-kura zuwa wurin da ta rataye su.
Kazalika, wani hoton bidiyo ya nuna hoton daya daga cikin mutanen wanda aka rubuta “Haka za mu rika yi wa masu garkuwa” a kirjinsa.
Tun bayan da ta karbi mulkin kasar ta Afghanistan a watan Agustan da ya gabata, kungiyar ta yi alkawarin yin mulki mai sassauci sabanin irin wanda ta yi a baya.
Tsohon Shugaban ’Yan Sandan Musulunci na Kasar, Mullah Nuruddin Turabi, wanda a yanzu kuma shi ne ke kula da gidajen kurkukun kasar cewar irin wadannan hukunce-hukuncen za su ci gaba a kasar saboda tabbatar da tsaro.
Ya ce za a ci gaba da yi a baiwar jama’a kamar yadda aka yi a baya, inda ya ce babu wanda zai fada musu yadda dokokinsu za su kasance.