Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana bukatar kayan agaji da tallafi na Dala biliyan biyar domin kawar da bala’i da ya auka wa kasar Afghanistan a shekarar 2022.
Tallafin na Dala biliyan biyar da ake nema domin Afghanistan shi ne mafi girma da Majalisar Dinkin Duniyar ta taba bukata domin wata kasa.
- Dalilin da na gudu tun kafin Taliban ta kwace mulki —Tsohon Shugaban Afghanistan
- Saudiyya ta aike da jiragen kayan tallafi zuwa Afghanistan
Da yake roko ga hukumomi da kungiyoyin kasashen duniya, Babban Jami’in Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths, ya ce, “Wani babban bala’i na tafe, don haka wannan sakon kar-ta-kwana ce; Ku taimaka, kada ku rufe kofar taimaka wa al’ummar Afghanistan; Ku taimaka a kawar da bala’in yaduwar yunwa da cututtuka da sauran bukatun rayuwa da ke iya haddasa mace-mace.”
Griffitths ya shaida wa wani taron manema labarai a birnin Geneva cewa rashin samun tallafin na iya nufin, “salwantar da rayuwa ta nan gaba”, a Afghanistan.
Ya bayyana cewa samun kudaden da kayan tallafin zai taimaka wajen saukaka irin wahalhalun rayuwa da jama’ar kasar suka shafe kusan shekara 40 suna fama da su.
Daga cikin kudaden, a cewarsa, za a yi amfanin da Dala biliyan 3.9 wajen tallafa wa mutum miliyan 22 da ke cikin kasar Afghanistan; Dala miliyan 623 kuma za a yi amfani da su ne domin tallafa wa mutum miliyan 5.7 ’yan kasar da ke zaman gudun hijira a kasashen da ke makwabtaka da ita.
Tun bayan da Taliban ta karbe mulkin Afghanistan a tsakiyar watan Agustan 2021, kasar take ta tangal-tangal a bangaren tattalin arziki gami da hauhawar farashin kaya da rashin ayyuka.
Gwamnatin Amurka ta rufe asusun ajiya da kadarorin kasar Afghanitsan da ke kasarta, sannan ana fama da karancin kayan agaji a Afghanistan a halin yanzu.
Uwa uba, a 2021 kasar ta yi fama da karancin ruwan sama, wanda aka shafe shekaru masu yawan gaske ba a ga kamarsa ba.