Wani jirgin soji ya isa birnin Kabul na kasar Afghanistan domin kwaso mutum kimanin 200 da suka hada da Amurkawa da ’yan wansu kasashe, bayan gwamnatin Taliban ta amince da hakan.
Taliban ta amince ta bar mutanen su fice daga Afghanistan zuwa kasar Qatar ne bayan matsi da lallashi daga Wakili na Musamman na Amurka a Afhganistan, Zalmay Khalilzad.
- An kai hari gonar Obasanjo an yi gakuwa da ma’aikata
- Allah ya yi wa Sarkin Sudan na Kontagora rasuwa
Akwai wasu Amurka masu jiragen kashin kansu dai da suka makale a Mazar-i-Sharif na Afghanistan, saboda Taliban ta hana jiragensu tashi; kawo yanzu kuma babu tabbaci ko suna cikin mutanen da jirgin na ranar Alhamis zai kwasa zuwa Qatar.
Tun bayan kwace ikon Afghanistan da Taliban ta yi, da kuma janyewar dakarun Amurka a karshen watan Agusta, kasashen Amurkan da Birtaniya ke fadi-tashin kwashe mutanen ke son ficewa daga kasar.
A kan haka ne Birtaniya ta bullo da wani sabon tsari da zai ba wa tsoffin ma’aikatanta ’yan Afghanistan damar ficewa.
Sai dai kawo yanzu da dama daga cikon tsoffin ma’aikatan na ci gaba da zaman jiran gwamnatin Birtaniya ta amince da bukatarsu a karkashin tsari.
Akwai kuma wadanda ba wadanda aka yi watsi da bukatarsu da kuma wadanda aka amince musu amma babu halin su fice daga Afghanistan.
A ranar Laraba wani tsohon mai tafinta a Afghanistan ya ce dakaru na musamman akalla 400 da Amurka ta horar a kasar suna zaman buya a halin yanzu Afghanistan.