Comoros ta yi waje da tawagar ‘yan wasan kasar Ghana daga gasar cin kofin Afirka bayan lallasa ta da kwallaye 3 da 2 a karawarsu a daren ranar Talata.
Ghana ta karkare wasan da ‘yan wasa 10 bayan bai wa Kyaftin dinta, Andre Ayew jan kati a minti na 25.
- Wutar lantarki ta babbake barawon wayar transfoma
- Daga Laraba: Hanyoyin Warware Matsalolin Bayan Jefa Kuri’a
Rabon Ghana da ficewa daga gasar cin kofin Afrika a matakin rukuni tun a 2006 yayin da kuma rabonta da ta lashe kofin tun a 1982.
Comoros wadda yanzu ke matsayin ta 132 a jadawalin FIFA iya tsallakawa matakin gaba na gasar ta cin kofin Afrika na matsayin gagarumar nasara kuma bazata a gareta.
Yanzu haka Comoros ta koma matsayin ta uku a rukunin C, yayin da Morocco da kuma Gabon bayan rashin nasara a wasanni 2 da ta doka a Kamarun.
Kankanuwar kasar da ke da matukar rauni a kwallo, ta samu tikitin iya shiga gasar ta cin kofin Afrika ne karon farko a 2016 bayan yunkuri har sau 20.
Ficewar Ghana daga gasar zai kara zama matsin lamba ga mai horarwa Milovan Rajevac wanda ya karbi ragamar horas da tawagar ‘yan wasan kasar a watan Satumbar da ya gabata bayan karewar kwantiraginsa na farko.
Yanzu haka Ghana ta koma gida don shirye-shiryen tunkarar wasan cike gurbin da zai bata damar samun tikiti a gasar cin kofin Duniya, wasan da za ta kara da Najeriya, Senegal, Morocoo ko kuma Algeria.