✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON Final: Rigar Super Eagles ta yi ƙaranci a Kano

Farashin rigar ya yi tashin gwauron zabi a Kano.

Magoya bayan tawagar ’yan wasan Super Eagles a Jihar Kano, sun koka kan yadda rigar Najeriya ta yi tsada da ƙaranci a jihar.

Aminiya ta ruwaito yadda rigar ta yi ƙaranci a kasuwa saboda yadda dubban magoya baya suka yi tururuwar saye ta, don taya ‘yan wasan tawagar murna, da zarar sun kashe Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON).

A ranar Asabar kamar yadda Aminiya ta yi bincike, ana sayar da rigar kan Naira 5,000 amma zuwa wayewar ranar Lahadi aka koma sayar da ita 15,000 a jihar.

Wani magoyin bayan Super Eagles, mai suna Usman Muhammad, ya ce: “Maganar dana ke da kai yanzu na kasa samun ta a Kano, amma wani ɗan uwana ya min hanya a Kaduna za a kawo min ta.

“Dole sai mun tsadance kafin mu same ta, domin a cewarsa (ɗan kasuwar) suna sayar da ita Naira 20,000 zuwa 25,000 a Kaduna yanzu haka, ni dai ina jira a kawo min tawa zuwa yamma.”

A nasa bangaren, Junior Lukas, ya ce ya so ya saka rigar a daren yau (Lahadi), amma ba zai iya kashe kansa ba duba da yadda rigar ta yi tsada sosai.

“Gaskiya na so na sayi rigar amma tun da babu ita, ba zan iya saya ba ko da kuwa Naira 10,000 ake sayar da ita,” in ji shi.

Wasu rahotanni sun bayyana cewar ’yan kasuwa ne, suka boye rigar domin samun ƙazamar riba.

Super Eagles dai, na fatan lashe Kofin Cin Nahiyar Afirka (AFCON) karo na hudu, idan suka doke masu masaukin baki Ivory Coast a daren ranar Lahadi.