Dan wasan gaban Kasar Masar, Mohamed Salah, ya koma kungiyarsa ta Liverpool don yin jinya bayan raunin da ya samu a Gasar Nahiyar Afirka da ake bugawa a Kasar Ivory Coast.
Salah ba zai buga wasan da Masar za ta yi da kasar Cape Verde ba, sannan ba zai samu damar buga wasannin da tawagar za ta yi idan ta fito daga rukunin B na AFCON.
- Mutum 2 sun shiga hannu kan safarar yara 16 a Taraba
- NAJERIYA A YAU: Dabaru 10 Na Kaucewa Masu Garkuwa Da Mutane
Salah dai, ya zura kwallo daya a karawar da Masar ta yi da kasar Mozambique a bugun fanareti.
Dan wasan ya samu rauni a wasan da Masar ta yi da Ghana, inda aka yi canjin sa a minti na bakwai da fara wasa.
Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya bayyana cewar, Salah ya koma kungiyar domin yin jinyar raunin da ya samu.
Amma ya ce kofa a bude ta ke ga dan wasan idan ya warke kuma yana da bukatar komawa don taimaka wa kasarsa.
Salah dai, bai taba lashe gasar Nahiyar Afirka ba; sau biyu kasarsa na shan kashi a wasan karshe na gasar.
A 2017 Masar ta yi rashin nasara a hannun Kamaru, sannan a 2021 ta sake yin rashin nasara a hannun Senegal.
Amma Salah, ya bayyana kwarin gwiwarsa kan cewar kasarsa za ta lashe gasar AFCON ta bana.