A ranar Alhamis ce za a fafata wasan kusa da karshe na Gasar Cin Kofin Afirka tsakanin kasar Kamaru mai masaukin baki da kasar Masar a wasan da ake wa kallon wasa mafi zafi a gasar a filin wasa na Olembe da ke birnin Yaounde.
Kasar Kamaru mai masaukin baki tana matukar tashe a wannan gasar, inda ba ta rasa wasa ko daya ba tun fara gasar har zuwa wannan mataki na wasan kusa da karshe.
- An gano matattarar dillalan kwaya kusa da ofishin ’yan sandan Abuja
- Kisan Hanifa: An mayar da shari’ar gaban Babbar Kotu
A wasannin rukuni na A da kasar ke ciki, Kamaru ta samu nasara a wasa biyu, ta yi kunnen doki a wasa daya.
A wasan zagaye na biyu na farko, Kamarun ce ta doke kasar Comoros da ci biyu da daya, sannan ta doke Gambiya a wasan kusa da wasan kusa da karshe, inda ta yanki tikitin zuwa wasan kusa da karshe tare da Masar.
Baya ga rashin rasa ko wasa daya, kasar Kamaru ce ta fi kowacce zura kwallaye a gasar, inda zuwa yanzu ta zura kwallo 11 a ragar kasashen da ta fafata da su.
A dayan bangaren kuma, Masar ta fara gasar da kafar hagu ce, bayan da Najeriya ta doke ta a wasan farko na Rukunin D na gasar da ci daya da nema.
Sai dai a sauran wasannin rukunin guda biyu ta dage, inda ta ci duka biyun da ci daya da nema.
A wasan zagaye na biyu na farko, kasar ta doke kasar Ivory Coast ne a bugun fanareti, sannan ta doke Moroko da ci biyu da daya a wasan kusa da wasan da za su buga da Kamaru.
Sai dai kuma Masar ba ta kai kasar Kamaru zura kwallaye ba, inda a duka wasannin ta zura kwallo hudu kawai, inda aka kwatanta da kwallo 11 da Kamaru ta zura.
Vincent Abubakar da Karl Toko-Ekambi ne kawai suka zura kwallaye 11 da kasar Kamaru ta zura a gasar.
Kece raini tsakanin Salah da Vincent Abubakar
Masu kallon gasar suna ganin wasan zai zama wani lokaci na kece raini tsakanin Vincent Abubakar wanda ke jan zarensa a gasar a yanzu da kuma Mohammad Salah wanda fitaccen dan wasa ne da ake ganin zai dauki kasar Masar din a gasar.
Daga fara gasar zuwa yanzu, Vincent Abubakar ya zura kwallo shida, shi kuma Mohammed Salah na da kwallo biyu ne kacal.
Vincent Abubakar
Abubakar mai shekara 30 a yanzu yana taka leda ne a kungiyar Al Nassr ta Saudiyya, kungiyar da ya je a bara.
Da zuwansa zuwa yanzu ya buga wasa 14, inda ya zura kwallo 6.
A kakar 2020-2021, ya buga kwallo ne a kungiyar Besiktas ta Turkiyya, inda ya zura kwallo 15 a wasa 26.
A kasar Kamaru kuwa a zura kwallo 31 ne a wasa 82 da ya buga wa kasar.
A wannan gasar da ake yi a kasarsa, ya zura kwallo shida, inda yanzu haka yake jan ragamar wadanda suka fi zura kwallo a gasar.
Mai biye masa ma dan kasar Kamarun ne, wato Karl Toko-Ekambi wanda shi kuma yake da kwallo biyar.
Masu kallo suna ganin idan masu tsaron bayan Masar sun takura wa Abubakar, akwai Karl Toko-Ekambi, wanda shi ne ya zura kwallo da kasar Kamaru ta ci a wasansu na karshe kafin wannan wasa da za a fafata.
Mohammed Salah
Salah fitaccen dan wasa ne da a yanzu haka yake jan zarensa a kungiyar Liverpool a Firimiyar Ingila.
Ya kuma dade yana jan zarensa a Gasar Firimiyar Ingila din da Gasar Cin Kofin Afirka.
Sai dai ana ganin har yanzu bai warware ba a gasar ta bana, ganin kwallo biyu kawai ya zura har zuwa wannan lokaci da ake ciki.
Sauran wadanda suka zura kwallo biyu na kasar Masar din su ne Mohamed Abdelmonem da Trezeguet, inda kowannensu ya zura kwallo daya.
Sai dai masu sharhi na kallon Trezeguet a matsayin dan wasan gaba da zai iya kawo sakamako mai kyau a kowane lokaci a wasan, idan har Salah ya samu matsi daga ’yan wasan bayan Kamaru.
Dayan wasan, wanda shi ne za a fara, za a fafata ne tsakanin kasar Burkina Faso da Senega a ranar Laraba.
Hasashen ’yan wasan Masar da za su fara wasan
Kasar Kamaru ba ta da wata matsala a cikin ’yan wasanta, wanda hakan ya sa ake hasashen za ta zuba zaratan ’yan wasanta ne.
’Yan wasan su ne: Onana, Fai, Castelletto, Ngadeu, Tolo, Oum Gouet, Toko Ekambi, Kunde, Zambo Anguissa, Ngamaleu, Aboubakar.
Ita kuma Masar kuwa, dan wasanta na baya Ahmed Hegazi ya samu rauni mai girma, wanda ya sa ba zai kara buga wasa a gasar ba.
Haka kuma akwai matsala a golan Masar, inda babban golan kasar na daya, Mohamed El Shenawy, ya ji rauni a wasansu da Ivory Coast, inda golan kasar na biyu Gabaski ya canje shi.
A wasan kasar kuma da Moroko na karshe kafin wannan wasan, shi ma Gabaski ya samu rauni, inda golansu na uku, Mohamed Sobhi, ya canje shi.
Wannan ya sa ake hasashen ’yan wasan farko da za su fara wasan su ne: Sobhi, Kamal, Abdel Monem, Ashraf, Fattouh, El Solia, Elneny, Fathy, Marmoush, Mohamed, Salah.