Kungiyar Kwallon Kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta yi wa kasar Masar ci daya mai ban haushi a wasansu na farko a Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka ta bana.
Najeriya ta zura wa kungiyar Pharaohs ta kasar Masar ci daya a raga ne ta hannun dan wasanta, Kelechi Iheanacho.
- AFCON: Shin Najeriya za ta iya lashe Gasar Kofin Afirka?
- ISWAP ta kai hari garin su Burutai, ta hallaka mutane
Iheanacho ya zura kwallon ne a bayan minti 30 da fara wasan da ya gudana a kasar Kamaru.
Najeriya da kasar Masar na Rukunin D na gasar da aka fara gudanarwa a karshen mako.