Tawagar ’yan wasan Super Eagles ta lallasa kasar Guinea-Bissau da ci 2-0 a wasan karshe na Rukunin D a matakin farko na Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirkta ta 2021.
Tawagar ’yan wasan kasashen biyu sun barje gumi ne a daren ranar Laraba, a filin wasa na Roumdé Adjia da ke kasar Kamaru.
- Gwamna Matawalle ya kara nada sabbin hadimai 250
- An umarci Gwamnatin Tarayya ta biya Nnamdi Kanu diyyar Naira biliyan 1
An shafe minti 45 din farko ba tare da jefa kwallo a ragar kowace kasa ba.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne dan wasan Super Eagles, Umar Sadiq, ya zura kwallo a minti na 56.
Shi kuma Troost-Ekong, wanda shi ke rike da kambun Kyaftin din tawagar ya jefa kwallo na biyu a minti na 79.
Yanzu haka tawagar Super Eagles ce ke kan gaba a Rukunin D da maki tara, a yayin da kasar Masar ke biye mata a matsayi na biyu da maki shida.
Sudan ta kare a mataki na uku da maki daya, sai Guinea-Bissau, wadda ita ce ta karshe da maki daya.