Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta Super Eagles, Ahmed Musa, ya ba babban masallacin birnin Garoua da ke kasar Kamaru gudunmawar Dalar Amurka 1,500, kwatankwacin sama da N600,000 domin kammala aikin gininsa.
Rahotanni sun ce dan wasan dai ya bayar da tallafin ne yayin da ake ci gaba da fafata wasannin cin kofin Nahiyar Afirka wanda ke gudana yanzu haka a kasar.
- AFCON 2021: COVID-19 ta kama ’yan wasa 12 a tawagar Tunisia
- Matasa na zanga-zanga a Gashuwa bayan soja ya bindige direba
A cewar Adepoju Tobi Samuel, wani dan jarida da ke bibiyar al’amuran wasanni, Ahmed Musa tare da sauran ’yan wasa Musulmai daga wasu kasashen dai sun lura cewa masallacin birnin wanda ’yan wasan suke zuwa sallah ba a kammala shi ba.
Hakan, a cewarsa ya sa suka yanke shawarar yin kudi-kudi domin ba da tallafin kammala shi.
A cewar Adepoju, “Ahmed Musa ya ba da tallafin $1,500 ga aikin ginin babban masallacin birnin Garoua na Kamaru.
“Yan wasa da shugabannin tawagar tun da suka je birnin a masallacin suke salla.
“Tallafin zai taimaka wa aikin ginin masallacin, kuma masu kula da shi sun ji dadi sosai,” inji shi.