A yunkurin hayewa zuwa gasar cin Kofin Afirka da ake sa ran yi a kasar Kamaru a badi, kasar Libya ta mayar da wasan da za ta yi da Najeriya zuwa kasar Tunisiya. A farko an shirya wasan zai gudana ne a kasar Aljeriya amma saboda wasu dalilai kasar ta canja wurin wasan zuwa Tunisiya.
Kamar yadda jadawalin wasan ya nuna, wasan zai gudana ne a ranar Lahadi 14 ga watan gobe kwana hudu bayan kasashen biyu wato Najeriya da Libya sun kece raini a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna a ranar Laraba 10 ga Oktoba, 2018.
Tunda farko kocin Libya, wanda dan asalin Aljeriya ne Abdil Amrouche ya ba Libya shawarar ta kai wasan da za ta yi da Najeriya zuwa Aljeriya, amma daga baya sai kasar ta gwammace ta yi wasan a Tunisiya maimakon Aljeriya.
Kafar watsa labaran wasanni ta Completesport ta ce Libya ta canja ra’ayin buga wasanta na gida a Tunisiya ne maimakon Aljeriya saboda matsalar tsaro.
Kamar yadda Libya take fuskantar matsalar tsaro da hakan ya sa ta mayar da wasanta na gida zuwa wata kasa ta daban, hakan ne ya sa ta sake canja shawarar mayar da wasan zuwa Tunisiya saboda matsalar tsaro a Aljeriya, kamar yadda wani rahoto ya nuna.
Kawo yanzu Libya ce take samun teburi a Rukunin E da maki hudu sai Afirka ta Kudu ke biye da maki 4 sai Najeriya mai maki uku sai Seychelles wadda ba ta da maki ko daya.
Masoya kwallon kafa sun zuba ido su ga yadda wasan zai kaya don duk kasar da ta sake aka doke ta a wannan wasa, to za ta fuskanci matsala a kokarin hayewa gasar cin Kofin Afirka.
Rabon da Najeriya ta halarci gasar cin Kofin Afirka tun a shekarar 2013 a karkashin horarwar marigayi Stephen Keshi wanda ya samu nasarar lashe kofin.