✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON 2019: Gobe Najeriya za ta kece raini da Seychelles

A ci gaba da yunkurin hayewa gasar cin kofin Afirka, a gobe Asabar ne idan Allah Ya kaimu, kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za…

A ci gaba da yunkurin hayewa gasar cin kofin Afirka, a gobe Asabar ne idan Allah Ya kaimu, kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta hadu da takwararta ta kasar Seychelles.  Wasan zai gudana ne a can Seychelles da misalin karfe 1 da rabi na rana agogon Najeriya.

Najeriya dai tana fafawawa ne a rukunin E da kasashen Afirka ta Kudu da Libya da kuma Seychelles.

A wasan da Najeriya ta yi na farko da kasar Afirka ta Kudu, ta sha kashi ne da ci 2-0 a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Akwa Ibom.

Sannan Libya kuma ta lallasa Seychelles ne a wasan farko da ci 4-1 da hakan ya sa wasan na gobe zai yi zafi, ganin dukkan kasashen biyu suna neman samun nasara ne a wannan wasa don kada a yi musu sakiyar da babu ruwa.

Seychelles dai kasa ce da ke Gabashin Afirka, ta yi iyaka da tekun Indiya.  Sannan mutanenta ba su wuce dubu 95 ba.

Sai dai a harkar kwallon kafa, babu karamar kasa, don haka sai Super Eagles ta yi da gaske muddin tana so ta samu nasara.

Duk kasar da ta samu nasara a kowane rukuni ne za ta haye zuwa gasar cin kofin Afirka da ake sa ran zai gudana a Kamaru a shekarar 2019.

Rabon da Najeriya ta halarci gasar cin kofin Afirka tun a shekarar 2013.