✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Addu’ar dogara ga Allah

Na zo gare Ka, ya Ubangiji, domin Ka kiyaye ni. Kada Ka bari a yi nasara da ni. Kai Allah Mai adalci ne, Ka cece…

Na zo gare Ka, ya Ubangiji, domin Ka kiyaye ni. Kada Ka bari a yi nasara da ni. Kai Allah Mai adalci ne, Ka cece ni, ina rokonka! Ka ji ni! Ka cece ni yanzu! Ka zama mafakata, don Ka kiyaye ni, Ka zama Mai kare ni, don Ka cece ni. Kai ne mafakata da kariyata, Ka bi da ni yadda Ka alkawarta. Ka kiyaye ni daga tarkon da aka kafa domina, Kai ne inuwata. Ina ba da kaina gare Ka domin Ka kiyaye ni. Za ka fanshe ni, ya Ubangiji, Kai Allah Mai aminci ne. Kana kin wadanda suke yi wa gumaka sujada, Amma ni na dogara gare Ka. Zan yi murna da farin ciki, saboda madawwamiyar kaunarKa. Ka ga wahalata, Ka kuwa san damuwata. Ba Ka bar magabtana su kama ni ba, Ka kiyaye ni, Ka yi mini jinkai, ya Ubangiji. Gama ina shan wahala, idanuna sun gaji saboda yawan kuka. Na kuwa tafke kwarai! Bakin ciki ya gajerta kwanakina, Kuka kuma ya rage shekaruna. Na raunana saboda yawan wahalata, Har kasusuwana suna zozayewa! Magabtana duka suna mini ba’a, makwabtana sun raina ni, wadanda suka san ni kuwa suna jin tsorona, sa’ar da suka gan ni a kan titi sukan guje mini. Duk an manta da ni kamar matacce, na zama kamar abin da aka jefar. Na ji magabtana da yawa suna rada, razana ta kewaye ni! Suna kulla makarkashiya don su kashe ni. Amma a gare Ka na dogara, ya Ubangiji, Kai ne Allahna. Kana lura da ni kullum, Ka cece ni daga magabtana, daga wadanda suke tsananta mini. Ni, bawanKa ne, Ka dube ni da alherinKa, Ka cece ni saboda madawwamiyar kaunarKa! Ina kira gare Ka, ya Ubangiji! Kada ka bari a ci nasara a kaina! Ka sa a ci nasara a kan mugaye, Ka sa su yi shiru a Lahira. Ka rufe bakin makaryatan can dukkan masu girman kai da masu fariya, wadanda suke yi wa adalai maganar raini!

Abin al’ajabi ne irin tanadin da Ka yi wa masu tsoronka! Abin da kake aikatawa a gaban kowa kuma, Yana da ban mamaki. Kana kiyaye wadanda suke amincewa da kai. Ka ɓoye su a wurinka lafiya daga makircin mutane, A inuwa mai lafiya Ka ɓoye su daga zargin magabtansu. Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Gama Ya nuna mini kaunarSa mai ban al’ajabi, Sa’ar da aka kewaye ni, aka fada mini! Na ji tsoro, na zaci Ka jefar da ni ne daga gabanka. Amma Ka ji kukana sa’ar da na yi kira gare Ka ina neman taimako. Ku kaunaci Ubangiji, ku amintattun jama’arsa duka! Ubangiji Yana kiyaye masu aminci, amma Yakan hukunta masu girman kai da tsanani. Ku karfafa, ku yi karfin hali, dukkanku da kuke sa zuciya ga Ubangiji!

Allah ne kadai Mafaka

Ga Allah kadai na dogara, cetona daga gare Shi yake fitowa. Shi kadai ne Mai kiyaye ni, Mai cetona, Shi ne kariyata, Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam. Har yaushe dukkanku za ku fada wa wani don ku yi nasara da shi, kamar rusasshen garu, ko kuma dangar da ta fadi? Ba abin da kuke so, sai ku kaskantar da shi daga makaminsa na daraja, kuna jin dadin yin karairayi. Kuna sa masa albarka, amma a zuciyarku la’antarwa kuke yi. Ga Allah kadai na dogara, A gare Shi na sa zuciyata. Shi kadai ne Mai kiyaye ni, Mai cetona, Shi ne kariyata, Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam. Cetona da darajata daga Allah ne, Shi ne kakkarfan Makiyayina, Shi ne Mafakata. Ya jama’ata, ku dogara ga Allah a kowane lokaci! Ku fada maSa dukkan wahalarku, Gama Shi ne Mafakarmu. Talakawa kamar shakar numfashi suke, Manyan mutane, su ma haka suke marasa amfani. Ko an auna su a ma’auni, sam ba su da nauyin komai, sun fi numfashi shakaf. Kada ku dogara da aikin kama-karya. Kada ku sa zuciya za ku ci ribar komai ta wurin fashi. In kuwa dukiyarku ta karu, kada ku dogara gare ta. Sau daya Allah Ya fada, Sau biyu na ji, cewa Allah Yake da iko. Madawwamiyar kauna, ta Ubangiji ne. Kai kanka, ya Ubangiji, Kake saka wa kowane mutum bisa ga ayyukansa.

Sa zuciya ga Allah

Ya Allah ! Kai ne Allahna, ina sa zuciya gare Ka. Duk niyyata ta nemanka ce, Raina yana kishinka, kamar bussasshiyar kasa, wadda ta zozaye, ba ta da ruwa. Bari in gan Ka a tsattsarkan wurinKa, in dubi daukakarKa da darajarKa. Madawwamiyar kaunarKa ta fi rai kansa, saboda wannan zan yabe Ka. Muddin raina, zan yi maka godiya, zan ta da hannuwana sama, in yi addu’a gare Ka. Raina zai yi liyafa, ya koshi sosai, ni kuwa zan rera wakokin murna na yabo a gare Ka. Sa’ar da nake kwance a gadona na tuna da Kai, Dare farai ina ta tunawa da Kai, Domin Kai Kake taimakona kullaum. Da murna, nake rera waka, a inuwar fika-fikanKa, Raina yana manne maKa, IkonKa yana rike da ni. Wadanda suke kokari su kashe ni, za su gangara zuwa Lahira, Za a kashe su cikin yaki, kyarketoci kuwa za su cinye gawarwakinsu. Sarki zai yi farin ciki ga Allah, duk wadanda suka yi alkawari da sunan Allah za su yi murna, amma za a rufe bakunan makaryata.