✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Addu’a (6)

Addu’ar roko daga wurin Ubangiji 1 Tarihi 4:9-19 “Yabez ya fi sauran ’yan uwansa kwarjini saboda haka mahaifiyarsa ta sa masa suna Yabez, wato da…

Addu’ar roko daga wurin Ubangiji

1 Tarihi 4:9-19

“Yabez ya fi sauran ’yan uwansa kwarjini saboda haka mahaifiyarsa ta sa masa suna Yabez, wato da wahala ta haife shi. Yabez ya roki Allah na Isra’ila, ya ce, “Ka sa mini albarka, Ka fadada kan iyakata, hannunKa kuma Ya kasance tare da ni, Ka kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni.” Allah kuwa Ya biya masa bukatarsa.”

Godiya ta tabbata ga Ubangiji Allahnmu Mai girma, domin wannan babban zarafi da Ya b amu don mu yi bincike cikin maganarSa. 

A wannan makon za mu yi nazari ne a kan addu’ar roko ga Ubangaiji. Kamar yadda muka gani cikin karantunmu da farko, inda bawan Allahn nan, Yabez, ya roki Ubangiji cikin addu’a don Ya sa masa albarka, Ya kuma fadada masa iyakarsa da kuma kasancewar hannuwan Ubangiji bisansa, sanan ya roki Ubangiji da Ya kiyaye shi daga macuta. Wannan abu ne da za mu yi koyi da shi wurin yin addu’ar roko daga wurin Ubangiji. Addu’ar rokon muna tsayawa a kan biyan bukatunmu ne kawai ko kuwa muna kara neman Ubangiji Ya sanya hanuwanSa bisa abubuwan da Ya tanada mana? 

 Za mu ga cewa bukatar mutane da dama a yau ita ce ne kudi. Babu shakka kudi abu ne mai kyau amma ba shi ne abu mafi muhimmanci a rayuwar dan Adam ba. Komai yawan kudin mutum idan bai nemi albarkar Ubangiji da kiyayewarSa ba, babbar matsala ce da damuwa ga rayuwa. Ba sai an gaya mana ba, akwai masu kudi da dama da ba su da albarkar Ubangiji bisansu, kuma muna ganin yadda irin wannan rayuwar take kasancewa; lalata, maye, mugunta da makamantansu. Shi ya sa a cikin karatun da muka yi mun ga cewa albarka da kariyar Ubangiji cikin komai su suka fi muhimmanci a koyaushe. Mece ce bukatarka a wurin Ubangiji? Kana rokonSa domin biyan bukatu ne kadai ko kuwa har da bishewarSa?

Allah daya ne, Shi kadai ne ke da iko bisa rayuwarmu, Shi kadai ne kuma Mai biyan bukatunmu. Shi ya sa yana da muhimmanci kwarai da gaske mu nemi fuskarSa ta wurin yin addu’a don mu iya mika rokonmu gabanSa don ya albarkace mu sa’annan Ya sanya mana kariya kan albarkar da ya tanada mana. Yabez ya roki Ubangiji Ya biya masa bukatunsa amma idan muka lura, bai tsaya a kan bukatunsa na jiki kadai ba amma ya roki Ubangiji Allah Ya sa masa albarka Ya fadada iyakarsa da Ya kuma kiyaye shi daga duk abin da zai cuce shi. Mukan yi tunanin cewa idan muka samu biyan bukata za mu iya kula da kanmu, bukatunmu na jiki ba su ne garkuwar rayuwarmu ba, amma idan muka roki bishewar Ubangiji cikin komai. Ubangiji Allah Mai jinkai ne Mai alheri ne kuma Yana cike da kauna a koyaushe ga duk wanda ke bidar fuskarSa. Saboda haka, a duk lokutan da muka zo gabanSa da roko, mu roki nasa nufin ga rayuwarmu, gama nufin Ubangiji Allah a gare mu alheri ne, cike da albarka da za mu ci moriyarta har abada. Ubangiji ba mutum ba ne da zai ce mun cika roko da yawa domin a duk lokutan da muka roke Shi Ya kuma biya mana bukatu muna kara damunSa da Ya kula da abubuwan da Ya tanada mana. Sam, rokon bishewar Ubangiji bisa albarkarSa zuwa gare mu, na nuna daukaka da girma da daraja sun tabbata a gare Shi ne kadai, domin Shi kadai ke da ikon tanadawa da kariya bisa komai, Yana kuma jin addu’ar ban-gaskiya a duk lokacin da muka kaskantar da kanmu a gabanSa, gama mutum ba ya da ikon kansa cikin komai. Kamar yadda Daniel ya yi addu’a ga Ubangiji a cikin Littafin Daniyel 9:18b-19, “Ba cewa muna da wani adalci na kanmu shi ya sa muka kawo roke-rokenmu ba, amma saboda yawan jinkanKa. Ya Ubangiji, Ka ji mu. Ya Ubangiji, Ka garfarce mu. Ya Ubangiji, Ka saurare mu, Ka yi wani abu saboda sunanKa. Ya Allahna! Kada Ka yi jinkiri domin da sunanKa ake kiran birninKa da jama’arKa.” 

Marubucin Zabura ma ya kara haske a kan yadda Ubangiji ne kadai Mai jin rokonmu da kuma bishewa, ya ce a duk lokacin da ya yi addu’a, yakan jira amsa daga wurin Ubangiji, wato nuna ban-gaskiya ga Ubangiji Mai biyan bukata. Zabura 5:3, “A gare Ka zan yi addu’a, ya Ubangiji! Da safe za Ka ji muryata da hantsi zan yi addu’ata, in kuma jira amsa.” Sa’anan idan muna neman nasara cikin shiye-shiryenmu: Karin Magana 16:3, “Ka roki Ubangiji, Ya sa albarka ga shirye-shiryenka, za ka kuwa yi nasara cikin aikata su.” 

Saboda haka, sai mu lura a duk lokutan da muke roko a wurin Ubangiji, mu zama da sanin cewa neman jagora da kariyarSa bisa bukatunmu na da muhimmanci kwarai da gaske. 

A bin farin ciki ne kwarai da gaske yadda Ubangiji Yake amsa addu’ar masu dogara gare Shi cikin gakiya. Ina fatan za mu juyo ga Ubangiji cikin addu’a don mu samu albarka da bishewarSa cikin rayuwarmu. 

Bari Ubangiji Ya bishe mu, amin.  

Ishaya 55:6, “Ku juyo wurin Ubangiji, ku yi addu’a gare shi, yanzu da yake kusa.