✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Addini yana koyar da zaman lafiya ne – Rabaran Tutu

Shugaban Cocin Assemblies of God na Gundumar Saminaka da ke Jihar Kaduna, kuma wakilin Shugaban Cocin Assemblies of God na Najeriya a yankin Arewa maso…

Shugaban Cocin Assemblies of God na Gundumar Saminaka da ke Jihar Kaduna, kuma wakilin Shugaban Cocin Assemblies of God na Najeriya a yankin Arewa maso Yamma Rabaran Haruna Tutu ya ce addini yana koyar da zaman lafiya ne.

Rabaran Haruna Tutu ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen taron da cocin ya shirya don murnar cika shekara daya  da sake bude cocin da asibitoci da makarantunta da aka gudanar a kauyen Kwanar Bakoshi a kusa da garin Saminaka.

Ya ce idan mutum ya samu ilimin addini, zai san yadda zai yi mu’amala da jama’a da kuma yadda zai zauna lafiya da su. Ya ce don haka ya kamata shugabannin addini su rika koya wa jama’arsu yadda za su yi tafiya da jama’a da yadda za su zauna lafiya da makwabtansu.

“Abin da na koya ke nan, kuma a kullum abin da nake koya wa jama’a ke nan. Mutum ba zai iya addini ba, idan ba ya zaman lafiya da makwabtansa. Don haka nake zaune lafiya da makwabtana,” inji shi.

Rabaran Tutu ya yi bayanin cewa babban abin da suka sanya a gaba shi ne ci gaba da kiran ’yan uwansu da suke jayayya da su har yanzu, kan su zo a hada kai domin a ciyar da wuraren cocin da aka sake budewa gaba domin al’umma su amfana da wuraren.

A jawabin Babban Bako, Esu Jukwai daga Abuja Cif Bawa Jeta ya bayyana cewa tun farkon wannan rikici, a matsayinsa na uba ya yi iyakar kokarinsa wajen ganin an sasanta bangarorin cocin biyu, amma abin ya gagara.

Ya ce lokacin ya rubuta wa Majalisar Shugabannin Cocin na Kasa takarda, kuma ya tara dukkan bangarorin biyu a fadarsa ya yi musu nasiha kan su yi hakuri su tafi tare. Amma daya bangaren ya ki ya tafi kotu. Daga karshe kuma suka zo ba su samu nasara ba a kotun.

“A yau wdanasu daga cikin masu wannan jayayya Allah Ya juya ra’ayinsu sun dawo. Za mu ci gaba da bin wadannan mutane muna rokonsu kan su dawo domin a zama daya a wannan coci. Za mu zagaya kasar nan baki daya, don ganin mun gudanar da wannan aiki. Muna kira mu yi hakuri da juna, mu zamo daya mu yi tafiya tare, domin babu kyau mu ci gaba da tafiya rarrabe a wannan coci,” inji shi.

A jawabin tsohon Shugaban Matasan Cocin na Kasa, Rabaran Paul Nathan Udeze ya bayar da hakuri ga Shugaban Cocin na Shyiyar Saminaka Rabaran Haruna Tutu, kan abubuwan da suka yi masa.

Ya ce su ne suka shirya dukkan matsalolin da aka samu a wannan shiyya ta Saminaka. Don haka ya zo wannan taro domin ya roki a gafarta masa. Daga nan ya yi kira ga mabiya wannan coci a shiyyar, su hada kai su zauna lafiya.