Gwamnatin Jihar Kano ta ce babu gudu ba ja da baya a kokarinta na ciyo bashi domin aikin ginin titin jirgin kasa a jihar.
Kwamishinan Yada labarai, Muhammad Garba a martanisa ga barazanar da kungiyar Kwankwasiyya ta yi, ya ce sai da suka tattauna da duk masu ruwa da tsaki a jihar kafin su dauki matakin.
Ya ce babu wata adawa da za ta sa su janye daga aikin a kokarin da suke yi na mayar da Kano hamshakin birni.
“Baya ga sauran amfanin da za a samu, aikin layin dogon zai bunkasa harkokin kasuwanci, ya saukaka harkar sufurin kayan amfanin gona daga kowane sashe na jihar”, inji kwamishinan.
Ya kara da cewa tun da Bankin Shige da Fice na kasar Sin ya riga ya amince da bukatarsu ta bada rancen, gwamnatinsu ba ta da wani zabi da ya wuce na karbo kudaden don aiwatar da aikin.
Muhammad Garba ya ce gwamnatin jihar ta bi dukkan matakan da suka kamata wajen ciyo bashin kama daga samun amincewar Majalisar Dokokin Jihar da kuma da kuma dukkan hukunmomin Gwamnatin Tarayya da suke da hakki kan lamarin.
Kwamishinan ya ce ko da dai bai yi mamakin matakin na kungiyar ta Kwankwasiyya ba, kasancewar ba ta taba yaba kowane irin aiki da gwamnatin APC ta kuduri aniyar aiwatarwa ba komai kyawunsa.