Mu tambayi kawunanmu haka shugabanninmu na yanzu suke? Wa ya isa ya tambayi Shugaban kasa ko Gwamna ko shugaban karamar hukuma da sauran mukarrabansu kan yadda aka yi suka samu suturun da suke fancamawa a cikinsu? Ba sutura ba, wa zai iya tuhumarsu kan motocin garari da suke shiga? Wa zai tuhume su kan dankara-dankarar motocin da ’ya’ya da matansu suke gasar saye? Yaya batun gidajen Mahadi ka ture da suke ginawa? Shin ma unguwanninku daya ne da na shugabannin? Shin makaranta daya ’ya’yanku da na masu mulki suke zuwa? Kasuwanni suke zuwa cefane ko kuma manyan shaguna (shopping malls)? Yaya asibiti, iri daya kuke zuwa da masu mulki?
Mu waiwaya baya kaso biyu kawai aka ga Sayyidina Umar (RA) da shi na suturar da shi ya rarraba wa sauran Musulmi na ganimar yaki da aka samu, amma aka tuhumce shi, kai aka ce ma ba za a saurare shi ba, ba za a yi masa da’a ba, sai ya yi bayanin yadda aka yi ya fi sauran Musulmi da sutura daya!
Kada mu manta kasar da yake mulki a lokacin ta hade Gabas ta Tsakiya da wani bangare na Asiya da Afirka. A yanzu ba za su gaza kasashe 30 zuwa 50 ba, amma riga daya ta jawo masa tuhuma daga talakan da yake mulka!
“Lallai Ubangijinka Yana nan a madakata.” (Alfajri).
Gwamna mai zafin rai:
Wata rana Umar (RA) ya zauna a gidansa a Madina yana jirar isowar wasu shugabannin kabilu da aka mika masa sunayensu domin nada daya daga cikinsu a matsayin gwamna. Sannanne ne cewa ba abu ne mai sauki ka zabi mutumin da zai zama gwamna ba. Koda an san mutum a matsayin gogagge kuma mai basira ba kowane lokaci ba ne za a samu ya hada wadancan halaye da saukin hali da tausayi.
Can kuwa sai daya daga cikin mutanen ya iso cikin kyakkyawar shiga abar burgewa. Ya ce: “Assalamu alaikum warahmatullah.” Umar ya lura yana da alamu irin ta sarakuna kuma ya yi shiga abar yabawa kuma samye da rawani kyakkyawa.
Amirul Muminina Umar bin Khaddabi ya ce masa ya zauna, kuma bai bata lokaci ba ya zauna a kan tabarma kusa da Umar (RA), ya debi dabino daga cikin wanda aka tanada domin baki ya ci. Bayan tattaunawa da shi na wani lokaci sai Umar (RA) ya gamsu cewa wannan zai iya zama shugaba mai fasaha da wayo wanda ya dace da wannan mukami na Gwamna.
Bayan lokaci kadan d agama tattaunawarsu sai mutum na biyu ya fado musu a jigace ya iso cikin sauri yana neman gafara kan rashin zuwansa a kan lokaci, a yayin da yake karkade kurar da ta mamaye suturarsa da gyara rawaninsa wanda ya karkace zuwa daya dag cikin kunnuwansa. “Ya Amirul Muminina! Ka gafarce ni kan rashin isowa da wuri. Ka gani a hanyata ta zuwa nan, na hadu da wata tsohuwa ce da jakinta. kafar jakin ya makale a tsakanin wasu duwatsu biyu.. ba zan iya wucewa ba ba tare da na taimaka mata ba.. ina tabbatar maka aiki ne mai wahala… don haka ina jin tsoro domin na dan makara.”
Umar (RA) ya karbi neman afuwarsa sannan ya nuna masa cewa ya kwantar da hankalinsa, yayin da abokin takararsa ya yi dariya ya ce, “To yanzu in tambaye ka wanne ne ya fi muhimmanci, kujerar gwamna ko kafar jakin?”
A daidai wannan lokaci sai daya daga cikin ’ya’yan Sayidina Umar (RA) ya fito da gudu daga daki ya fada ka cinyoyin Umar (RA). Sai Umar (RA) ya rungume shi da hannuwansa ya sumbace shi har sau biyu a kansa.
Mutum na farko sai ya gaza boye kunyarsa da rashin jin dadinsa da ganin haka. Sai ya ce: “Ban taba yin haka ba ya Amirul Muminina. ’Ya’yana goma ba su ma isa su zo kusa da ni ba, kuma hakika ban taba sumbatarsu ba.”
Umar (RA) ya zuba wa mutumin nan ido ya kada kansa, sannan ya ce: “Babu wani abu da zan iya yi a kan haka. Idan Allah ya kekasar da zuciyarka ta ki yin kirki. To amma ka tuna Allah Yana tausaya wa wanda ya nuna tausayawa ga halittunSa.”
Sai kuma Umar ya lura mutum na biyu yana murmushi tare da jin kunya, sai ya tambaye shi abin da ya faru.
Sai mutumin ya ce: “Ka gani ya Amirul Muminina! Ina da matsala sabanin haka. Ina da ’ya’ya biyar amma a koyaushe suna fado min a jiki. Kafin ma in taho karamarsu mai suna Laila ba ta so in taho ba… ta yi ta makale min tana bukatar in dauke ta, wannan ne ya sa ta bata min riga da kura.”
Sai Umar (RA) ya yi murmushi ya kalli sakatarensa wanda ke jirar ya ji daga Umar (RA) wane mutum ne ya yanke shawara a kansa. “Rubuta wa wannan mutum na biyu wasikar nada shi Gwamna, ina da yakinin shi ne ya dace da wannan aiki,” inji Umar (RA).
Mutumin nan na farko na jin shawarar da Umar (RA) ya yanke, nan take ya fara tari.
Sai Umar (RA) ya ce da mutumin nan na farko: “Ka gani, bai zai yiwu ka zama shugaba ba, kuma kana mutum mai alfahari. Shugaban kabilar da ya zama Gwamna yana da tausayi kuma zai so ya dauki lokacinsa yana taimakon wasu. Wannan mutumin kirki ne, kuma tunda ya zo nan yake nuna min yana da wadannan halayen kirkmi biyu.”
Wannan mutum na biyu wanda da kyar ya iya dakatar da tarin da yake yi, ya yi ta kokarin ya gano abin da Umar (RA) yake magana a kai, amma tunda Allah Ya takura zuciyarsa haka ya tafi ba tare da ya fahimci abi da ya say a rasa wannan kuejra ta Gwamna ba ga mutumin da ya zo da riga mai kura wanda ya damu kansa da yara da jakuna da tsofaffin mata.
Daga wannan kissa za mu fahimci shugabanci yana bukatar mutumin da ya damu da al’amuran mutanen da zai shugabanta ne ba mutumin da ya damu da yin ado ko sanya sutura na alfahari ba. Shugabanci na bukatar mutum mai tausayin na kasa da shi, mai taimakon raunana mai jinkan wadanda suka shiga matsala.
Mu dubi yadda mutumin da ya zama gwamna a karshe ya tsaya taimakawa wa tsohuwar da jakinta ya samu matsala a tsakanin duwatsu biyu.
Don haka duk mutumin da bai damu da halin da jama’a suke ciki ba, bai damu da su rayu ko su mutu ba, bai damu da tsaron rayuka da dukiyarsu ba, bai damu da komai na inganta rayuwarsu ba, in ba inda zai yi sama da fadi da kudin talakawa ba, to wannan bai cancan ya zama shugaban jama’a ba. Idan kuma har aka kuskura a ba shi amanar shugabanci, to barna da fasadi za su faru a bayan kasa. Allah Kai muke roko Ka fi kowa sanin halin da wannan kasa take ciki, sakamakon mika mulki ga wawayen cikinmu wadanda ba su dauki rayuwar dan Adam da muhimmanci ba, Ka kawo mana dauki daga wurinka, Ka ceto mu daga mugun nufinsu. Duk wanda yake da hannun kan zubar da jinin bayinKa, Ya Allah Ka gaggauta kawar da shi, Ka murkushe shi ka turmuza hancinsa a kasa. Ya Allah duk wanda yake zubar da jinin bayinKa a kasar nan ko wane ne Allah Ka gaggauta yin maganinsa, Ka ceto bayinKa daga wannan mugun hali da suke ciki, ya Allah ba domin halinmu ba, amma domin kananan yara da dabbobi da tsofaffi da sauran salihan bayinKa.