Adadin mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren baya-bayan nan a ƙaramar hukumar Bokkos da ke Jihar Filato ya kai 52 kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana.
Hakan ya biyo bayan sake gano wasu gawarwaki 40 ne a ranar Laraba da Alhamis da daddare yayin da masu aikin ceto suka ci gaba da kutsawa cikin dazuka don nemo waɗanda suka ɓata.
- Boko Haram: An kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno
- Yadda aka yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a Bauchi
Shugaban Ƙungiyar al’adu ta Bokkos Cultural Development Council (BCDC) Vanguard, Farmasum Fuddang, ya shaidawa tashar Talabijin Channels cewa an yi jana’izar mutane 31 a ranar Alhamis tare da wasu yara biyar da suka ƙone ƙurmus a ƙauyen Hurti. An kashe wasu 11 a ƙauyen Ruwi, huɗu a ƙauyen Manguna tare da kashe mutum ɗaya a ƙauyen Daffo.
A cewar Ƙungiyar al’adu ta Vanguard, mazauna garin na jiran sakamako daga ci gaba da bincike da ceto mutanen da suka ɓata a ƙauyukan Hurti da Mbar.
Gwamnatin Jihar Filato ta yi Allah-wadai da hare-haren tare da yin kira da a kwantar da hankula saboda a halin yanzu ana ci gaba da ɗaukar matakan tsaro a yankunan da lamarin ya shafa.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a, kwamishiniyar yaɗa labarai da sadarwa ta jihar, Joyce Ramnap ta bayyana damuwarta game da sabbin hare-haren.