✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adadin wadanda suka warke daga COVID-19 a jihohin Najeriya

A yanzu wata shida ke nan bayan bullar cutar coronavirus a Najeriya, inda ta yadu a duk johohi 36 na kasar da kuma Birnin Tarayya.…

A yanzu wata shida ke nan bayan bullar cutar coronavirus a Najeriya, inda ta yadu a duk johohi 36 na kasar da kuma Birnin Tarayya.

Alkaluman da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya (NCDC), ta saba fitar duk rana, sun nuna cewa daga bullar cutar a kasar yanzu mutum 52,800 ne suka harbu.

Bayanan NCDC sun nuna cewa mutum 39,964 ne suka warke daga cutar bayan kamuwa yayin da mutum 1,007 suka riga mu gidan gaskiya.

Rumbun tattaro bayanai na Hukumar ya nuna cewa, an samu mutum 707 da suka warke daga cutar cikin sa’a 24.

Kididdigar da hukumar ta fitar a ranar Litinin ta nuna cewa, mutum 39,257 ne suka warke, yayin da washegari da ta kasance ranar Talata, adadin mutanen da samu waraka ya kai 39,964.

Ga jerin adadin mutanen da suka warke daga cutar a kowacce daga cikin jihohi 36 na kasar da kuma birnin Abuja da cutar ta bulla:

  • Legas – 15,214
  • Birnin Tarayya (Abuja) – 1,450
  • Oyo – 1,732
  • Edo – 2,252
  • Filato – 1,168
  • Ribas – 1,901
  • Kaduna – 1,832
  • Kano – 1,507
  • Delta – 1,518
  • Ogun – 1,447
  • Ondo – 1,305
  • Inugu – 852
  • Ebonyi – 921
  • Kwara – 740
  • Katsina – 457
  • Osun – 648
  • Abiya – 643
  • Borno – 646
  • Gombe – 605
  • Bauchi – 545
  • Imo – 187
  • Binuwai – 141
  • Nasarawa – 298
  • Bayelsa – 326
  • Jigawa – 308
  • Akwa Ibom – 220
  • Neja – 168
  • Ekiti – 125
  • Adamawa – 159
  • Anambra – 159
  • Sakkato – 138
  • Kebbi – 82
  • Taraba – 73
  • Kuros Riba – 63
  • Zamfara – 72
  • Yobe – 59
  • Kogi – 3