Mahukunta sun tabbatar da cewa adadin wadanda suka rika mu gidan gaskiya sakamakon guguwa mai karfin gaske da ta afka wa wasu sassan kasar Philippines ya zarta 200.
Wani kakakin ’yan sanda a kasar, ya shaida wa manema labarai a ranar Litinin din nan cewa akalla mutane 208 ne suka mutu, sannan mutum 52 sun bace bayan guguwar da ta yi barna a lardunan tsakiya da kudancin kasar a karshen makon jiya.
- Madrid za ta dauko Haaland, Pogba da Mbappe a watan Janairu
- Najeriya A Yau: Dalilan ‘rashin yanke wa masu laifi’ hukunci a Najeriya
Roderick Alba ya ce an jibge jami’an ’yan sanda domin gudanar da ayyukan agaji da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan da bala’in ya afku.
Fiye da rabin mutanen da aka sanar da mutuwarsu ta yi muni musamman a tsakiyar yankin Visayas wanda ya hada da lardin Bohol, wanda ya kasance yanki mai dauke da shahararrun wuraren yawon bude na kasar ciki har da wuraren ninkaya.
Guguwar da kwararru suka yi wa lakabi da Rai, sun bayyana ta a matsayin mafi muni cikin shekarar 2021 a kasar ta Philippines, wadda ta afka wa wasu tsibirai cikin gudun kilomita 195 a sa’a 1.
Bayanai sun ce kawo yanzu ta raba mutane fiye da dubu 490 da matsugunansu gami da tumbuke manyan turakun lantarki da bishiyoyi kafin ta koma Kudancin China a karshen mako.
Duk da cewa daga bisani guguwar ta rage gudun da yake yi zuwa kilomita 150 cikin sa’a 1, iskar ta zubar da ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda ya mamaye kauyuka gami da rushe gine-gine a yankunan da ta ratsa.
Kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, guguwar Rai ta yi barna mai yawa a lardunan Cebu, Leyte, da Surigao del Norte gami da sanannen wurin hawan igiyar ruwa na Siargao da tsibiri Diginat.