Mamallakin aladiyar da ta haihu mai suna Alfredo Cardinas Junior, ya firgita bayan da ɗaya daga cikin aladun nasa ta haihu yana kallo, inda ya ji sautin kukan ɗan aladen kamar na dan-adam kuma yake kama da na jaririn ɗan-adam.
Jaririn aladen mai siffar mutum yana daga cikin jarirai takwas da aladiyar Mista Cardinas ta haifa kuma babu wani daga cikinsu da aka rawaito cewa ya samu naƙasu.
Mai aladen, Alfredo Cardinas Jr, ya bayyana cewa ya firgita sosai a lokacin da aka haifar masa jaririn aladen mai fuskar mutum.
Ya bayyana cewa: “Na ji tsoro sa’ad da na fara ganin jaririn. Na kara gigicewa da na ji kukansa. Na ji kamar irin na jaririn dan-adam.”
An haifi jaririn aladen ne a gidan Alfredo a birnin Tanjay da ke kudu da Manila a kasar Philippines.
Bidiyon jaririn aladen yana kukan da ba a saba ji ba, ya janyo ra’ayoyin jama’a sama da miliyan 1.5 a shafin Fesbuk.
Bidiyon ya nuna aladen da fuska irin ta mutum, amma babu idanu.
Alfredo ya ce, ya dora jaririn aladen a kan bargo a kasa yayin da yake yunkurin motsa jikinsa.
Sannan aka dora shi a kan wani tsohon buhu yayin da yake faman numfashi.
Sai dai bai yi tsawon kwana ba, inda ya mutu sa’o’i hudu kacal da haihuwarsa.
Likitan dabbobi na yankin, Dokta Ma Christine Hope Dejadena, ta ce, ba kasafai ake samun alade daya tak da wata nakasa bayan haihuwa ba.
Sai dai ta yi hasashen cewa, mahaifiyar aladen ta yi ciki da wani nau’in halitta ta daban.
Ta ce: “Aladen ba za ta samu juna biyu daga wani nau’in halitta ta daban ba.”
Madadin haka, ana da tabbacin cewa, an haifi aladen da larurar haihuwa da ake kira ‘holoprosencephaly’, da take haifar da cutar kwakwalwa.
Likitan dabbobi Dakta Aris Miclat ya yi bayanin: “Wannan cuta ce ta haihuwa, wadda a zahiri nakasu ce ta haihuwa.
Jaririn na da cuta da take da alaka da kai da gangar jiki (cephalic), wanda gaban kwakwalwa yake kasa girma zuwa mataki biyu na (cephalic).”
Dokta Miclat ya yi imanin cewa, zai iya kasancewa, mahaifiyar ta harbu da sinadarai ko magungunan kashe kwari yayin da take da ciki, wanda zai iya shafi girman alade a cikin mahaifa.
Ya ce: “Kusan koyaushe, wannan larura ta musamman tana iya sanadiyyar mutuwa.”
Likitan ya kuma musa zargin cewa akwai yuwuwar cudanya tsakanin uwar aladen da dan-adam.
Alfredo ya ce, ba shi ne karon farko da wata daga cikin aladunsa ta haifi alade mai nakasa ba.
A baya yana da alade da aka haifa kamar yana da fuka-fukai, suna fitowa daga jikinsa.
Alfredo ya yi imanin cewa, dabbar ta kawo sa’a ga iyalinsa, saboda ya sami damar saka hannun jari a cikin harkar kiwon shanu da wayar salula jim kadan bayan haihuwarta.
Wani bincike ya gano kusan kashi uku cikin dari na aladu ana haifar su da larura ta haihuwa.
Akalla akan samu alade daya da larura a kusan kashi 17 na cikin dabbobin da ake haihuwa.
Yawancin wadanda ke da nakasar haihuwa sun mutu a cikin mako guda da haihuwa.