Wata mai suna Abby Domer Salle ’yar asalin ƙasar Philippines ta sha suka kan zargin cin zarafin dabbobi bayan da aka gan ta dauke da wani dan tsako mai rai a cikin ƙaramin kejin ƙarfe a kanta a kan titunan Manila babban birnin ƙasar.
Ƙwararrun al’adun Kawaii na ƙasar Japan sun ce yin hakan wani ‘salon raino ne da ake yi wa dan agwagwa a bakin ruwa’ kuma sananne ne sosai a Kudu maso Gabashin Asiya a shekarun da suka gabata.
- Hisbah ta ware wa ’yan jarida gurbi 50 a auren gata — Daurawa
- An tsinci gawar wata ɗaliba a cikin ɗaki a Kano
Ba a san asalin wannan salo na Abby ba, amma an danganta shi da fasahar masu zane. Akwai bambance-bambancen ra’ayi da yawa kan wannan salo a duk fadin duniya, amma a cikin mafi sauƙin tsarinsa ya hada da sanya ’yar agwagwa ta roba don yin ado a kan mutum.
Ita dai ’yar ƙasar Filifins din kwanan nan ta dauki wannan salo da ba a saba gani ba, kuma hakan ya dauki hankalin jama’a zuwa wani sabon matakin ban- mamaki ta hanyar sa dan tsako da ransa a keji tana yawo da shi a bainar jama’a a zaman hula.
Hotuna da bidiyo na Abby, matashiya ’yar ƙasar Philippines a shafukan sada zumunta na yaduwa a birnin Manila dauke da dan tsako mai launin rawaya a kanta ana ta yada su a shafukan Intanet a kwanakin nan, wanda hakan ya haifar da fushin masu kare haƙƙin dabbobi a duniya.
Koda yake Abby mai yiwuwa ta yi tunanin cewa tana yin haka ne a matsayin salon fasaha, sai dai hakan ya haddasa tare da haifar da muhawara game da rashin da’a a cikin al’umma.
“Wannan zaluntar dabba ce, akwai alamun wahalar da dan tsakon,” a wani sharhi da wani mutum ya yi a shafin TikTok.
“Ina fata ɗan tsakon yana raye,” wani ya rubuta.
Abby Domer Salle ta kasance wacce ta shahara a shafukan sada zumunta na zamani ne tana da sama da mabiya dubu 53 a shafin TikTok da mabiya dubu 28 a shafin Facebook.