Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, adadin mutanen da suka rasa muhallansu a sassan duniya ya zarta miliyan 114, adadi mafi girma da majalisar ta tattara a tarihi.
Babbar matsalar da ta raba mutanen da gidajensu a watanni shida na farkon wannan shekara ta 2023, ita ce tashe-tashen hankulan da ake fama da su a Ukraine da Sudan da Somalia da Myanmar da Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo har ma da rikici a Afghanistan.
- Majalisar Amurka ta yi fatali da ƙudirin janye dakarun ƙasar daga Nijar
- Yawan Falasdinawan da Isra’ila ta kashe a Zirin Gaza sun haura 7,000
Kazalika ibtila’o’in da aka samu na fari da ambaliyar ruwa da rashin tsaro sun taimaka wajen raba mutanen da gidajensu kamar yadda Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijra ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta bayyana.
Sanarwar UNHCR ta ce, yanzu haka hankalin duniya ya karkakata ne kan yakin da ake fama da shi a Zirin Gaza wanda ya cika da dimbin fararen hula, amma fa akwai rikice-rikice da dama da ke ci gaba da ta’azzara tare da raba mutane da muhallansu a sassan duniya.
Shugaban hukumar, Filippo Grandi ya zargi kasashen duniya da gazawa wajen magance tashe-tashen hankula da dama, yana mai bukatar samar da hadin kai don kawo karshen matsalar ta raba mutane da muhallansu tare da komar da su gida.
Grandi ya kuma ce, wani kaso na adadin mutane da suka rasa muhalli sun tsere daga gidajensu ne sakamakon matsalar take hakkin dan Adam da ake fama da ita a wasu sassan.
“Gazawar al’ummomin duniya wajen magance rikice-rikice ko hana aukuwar sabbi shi ne musabbabin rasa muhalli da kuma kara jefa wadanda lamarin ya shafe cikin zullumi.
“Dole ne mu yi wa kanmu karatun ta nutsu, mu yi aiki tare don kawo karshen rikice-rikice, wanda hakan zai bai ’yan gudun hijira da sauran mutanen da suka rasa matsugunansu su koma gida ko kuma su sake gina matsugunansu,” in ji Grandi.
Ya zuwa watan Yuni, adadin mutanen da aka tilastawa gudun hijira a duniya ya kai miliyan 110, wanda wannan wani kari ne kan mutum miliyan 1.6 da suka tsere daga muhallinsu a rahoton da aka fitar a karshen shekarar 2022.
Haka kuma, a tsakanin watan Yuni zuwa karshen watan Satumba, an kiyasta karin wasu miliyan hudu da aka tilastawa gudun hijira, wanda ya kawo adadin zuwa miliyan 114.
Rahoton na UNHCR bai kunshi alkaluman rikicin Isra’ila da Falasdinu ba wanda ya barke a ranar 7 ga Oktoba ba.