Fiye da mutane 1300 ne suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasar da ta afku a garin Gaziantep da ke kan iyakar Turkiyya da Syria.
Rahotanni daga Kudancin Turkiyya sun tabbatar da mutane fiye da 1300 sun mutu sakamakon girgizar kasar mai karfin maki 7.8 da ta afku a birnin Gaziantep da ke kan iyaka da kasar Syria.
- An binne gawarwakin mutum 71 da ’yan bindiga suka kashe a Katsina
- Ciwon Daji na kashe mutum dubu 700 duk shekara a Afirka —WHO
Alkalumma sun tabbatar da cewa kawo yanzu mutum 912 sun mutu a Turkiyya yayin da 467 suka riga mu gidan gaskiya a Syria
Girgizar kasar wadda ta yi nisan tafiyar kilomita 18 a karkashin kasa ta dauki tsawon minti goma tana rugugi.
A halin yanzu an tura masu aikin ceto daga Syria da kuma Turkiyya domin ci gaba da neman wadanda suka makale cikin baraguzan gine-gine.
Kimanin gine-gine 130 ne suka lalace sakamakon girgizar kasar a Turkiyya yayin da kafofin yada labarai a Syria suka ruwaito rushewar tarin gine-gine a Aleppo da kuma Hama.
Cibiyar Kiyaye Aukuwar Bala’o’i ta Syria ta bayyana girgizar kasar a matsayin mafi muni a tarihin cibiyar.
Hukumomi sun kuma ce an jiyo rugugi har a kasashen Lebanon, Gaza da tsibirin Cyprus da kuma Masar.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya mika sakon jajensa ga wadanda iftila’in ya rutsa da su.
Shugaba Recep Tayyib Erdogan na Turkiya ya sanar da aike jami’ai na musamman don bayar da kulawa da kuma aikin ceto wadanda ibtila’in ya rutsa da su.
Turkiyya dai ta ayyana dokar ta baci tare da kira ga mutane su dakatar da amfani da wayoyinsu, saboda masu aikin agaji su samu damar kai wa ga wadanda suka makale a cikin baraguzai.
Tuni kasashen Duniya suka fara mika wa kasashen biyu tayin kai musu dauki ciki har da Amurka da ta ce a shirye take ta kawo dauki ga wadanda ibtila’in ya shafa.
A 1999, irin wannan mummunar girgizar kasar ta yi ajalin mutane dubu 17.