✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ACF ta dakatar da shugabanta kan furta kalamai ba da yawunta ba

Ƙungiyar Tuntuɓa ta Dattawan Arewa wato Arewa Consultative Forum (AC) ta ce ta dakatar da shugaban majalisar ƙolinta, Mamman Mike Osuman dangane da wasu kalamai…

Ƙungiyar Tuntuɓa ta Dattawan Arewa wato Arewa Consultative Forum (AC) ta ce ta dakatar da shugaban majalisar ƙolinta, Mamman Mike Osuman dangane da wasu kalamai da aka alaƙanta da shugaban a wani taronta da ta yi ranar Laraba a Kaduna.

A wata sanarwa da ACF ta fitar ta musanta wasu bayanai da ke yawo cewa sun bayyana goyon bayan fito da ɗan takarar Shugaban Ƙasa daga yankin Arewa a 2027.

Cikin sanarwar da ACF ta fitar ta hannun Shugaba da Sakatare Cibiyarta ta Amintattu, Alhaji Bashir Muhammad Dalhatu da Alhaji Murtala Aliyu Wazirin Dutse — Matawallen Gombe, ta ce Mista Osuman ya yi wannan kalaman ne ba da yawunta ba.

Sanarwar ta ce Osuman ya yi furucin ne ba tare da tuntuɓa ko neman shawarwarin sauran jiga-jiganta ba, saboda haka ra’ayinsa ne ya faɗa amma ba da yawunta ba.

Sai dai ƙungiyar ta kuma ce yankin na Arewa na fama da ƙangin talauci da matsalar tsaro da rashin ilimi, inda ta bayyana cewa gundarin matsalar yankin na hannun ‘yan Arewa.

Ƙungiyar ta bayyana cewa an jirkita bayanan ta wata fuskar da ba ita ce alƙiblar da ta ɗauka ba, tana mai nuna damuwa game da yadda yankin na Arewa ya samu kansa a koma baya musamman a fannonin da suka shafi ilimi da tattalin arzki da kuma talauci, sai kuma uwa-uba matsalar tsaro.

Waɗannan kalaman na zuwa ne bayan da aka samu wasu bayanai da wasu kafofi suka wallafa da ke cin karo da juna da aka alaƙanta da Mamman Mike Osuman, da aka ce ya faɗi cewa lokaci ya yi da yankin ya dace ya fito da shugaban da zai jagoranci Najeriya a shekarar 2027, da kuma ya san zafin al’ummarsa.