✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

AC Milan ta dauki Oliver Giroud daga Chelsea

Dan wasan zai zauna a kungiyar har zuwa 2023.

Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan ta sanar da kammala daukar dan wasan gaban Chelsea, Oliver Giroud mai shekara 34.

Giroud zai sanya riga mai lamba 9 a AC Milan, bayan barin Chelsea inda ya lashe Gasar Zakarun Turai a karshen kakar wasanni ta bana.

Dan wasan ya je Chelsea a 2018 bayan barinsa Arsenal, inda ya zura kwallo 39 a wasanni 119 da ya buga mata.

Ya kuma lashe Gasar cin Kokfin FA, Gasar Europa da kuma Gasar Zakarun Turai.

Dan wasan dan asalin kasar Faransa ya buga wa kasarsa wasanni 110 sannan ya zura kwallo 46.

Giroud ya rattaba hannu cewa zai shekara biyu a AC Milan har zuwa karshen kakar wasanni ta 2023.