✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abun fashewa ya yi ajalin Almajiri dan shekara 11 a Gombe

Mutum shida sun ji rauni.

Wani Almajiri mai shekaru 11 ya yi gamo da ajalinsa sanadiyyar wani abun fashewa a garin Abdullahi Dadin Kowa da ke Karamar Hukumar Yamaltu Deba ta Jihar Gombe.

Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ce ta tabbatar da hakan ta bakin kakakinta, ASP Mahid Mu’azu Abubakar.

ASP Mu’azu ya ce Almajirin ya rasa ransa ne ta hanyar wasa da wani abun fashewa da ba a tantance ko mene ne ba da kuma inda ya tsinto shi.

Ya ce yanzu haka jami’an ’yan sanda na sashin warware bama-bamai na ci gaba da gudanar da bincike kan burbudin karfen abun fashewar don gano ko mene ne.

Malami Almajirin wanda wakilinmu ya tattauna da shi, ya bayyana cewa sun rabu da Ali ya tafi bara amma bai wuce mintuna 15 ba sai labarin ya iske su cewa wani abu ya fashe a hannun sa kuma ya guntule masa hannu.

Malamin mai suna Muhammad Bello, ya bayyana cewa wani Almajirin sa ne ya same shi har gida ya sanar da shi faruwar lamarin.

A cewarsa, jin haka ne ya sanya ya hau babur zuwa ofishin ’yan sanda wanda da isarsa aka sanar da shi cewa an tafi da shi Gombe kuma a kan hanya rai ya yi halinsa, wanda dole aka dawo da shi suka yi masa jana’iza.

Wani da abun ya faru akan idonsa, Muhammad Barde, Wakilin Garin na Dadin Kowa, ya ce Almajirin shi kansa yana wasa da abun bai san cewa abun yana da hatsari ba a kusa da shi a gindin wata bishiya har barci ya dauke shi.

Barde ya bayyana cewa, yana tsammanin Almajirin ya dauki abun ne a kan zai kai wa ’yan jari Bola ashe shi ne zai zama silar ajalinsa.

Ya bayyana cewa, sun kai Almajirin asibiti a garin Hina amma ba a karbe shi, wanda a dalilin haka suka yi wa ’yan sanda waya a Gombe suka zo suka dauke shi kafin su karasa asibiti ya rasu.

Shi ma wani da lamarin ya shafa har ya ji rauni a kafarsa, Malam Tukur Hassan, cewa ya yi yana zaune yaron ya zo ya same shi yana wasa da abun a lokacin da barci ya dauke shi, sai kawai ya ji wani abu ya yi kara, kuma a nan ne ya tashi ya ga ya yi rauni a kafa.

Tukur ya ce su shida abun ya shafa sai dai kuma Almajirin ne kadai Allah Ya yi masa rasuwa kafin a karasa da shi asibiti.