Mazauna yankin Badarawa a Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, sun shiga rudani yayin da wani abun fashewa ya jikkata yara uku a yankin.
Wani dan uwan yaran da lamarin ya ritsa da su mai suna Umar, ya ce duk cikin yaran babu wanda ya haura shekara 8 a duniya.
- Abin da ya sa na cire dana daga makarantar gwamnati – El-Rufa’i
- Yawan mutanen da COVID-19 ta kashe a Indiya sun haura 400,000
“Lamarin ya yi muni saboda daya kasancewar daga cikinsu an yanke mai hannaye yayin da daya kuma idonsa guda ya samu matsala, amma dayan a yanzu yana samun sauki.
“Yaran sun shaida mana cewa wani ne ya basu robar lemon ‘Bobo’ su yi wasa da ita, inda ana tsakar haka ta fashe” a cewarsa.
Umar ya ce bayan aukuwar lamarin ne aka garzaya da su Asibitin Barau Dikko don ba su agajin gaggawa.
Aminiya ta ruwaito cewa har yanzu ba a samu masaniyar wanda ya ba su robar lemon ‘Bobo’ da ta kusa yin ajalinsu.
Kakakin ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce basu da masaniyar mene ne a cikin robar.
A cewarsa, sun tura jami’an dakile harin bam don yin bincike a wurin da abun ya faru.
“Muna jiran rahotonsu, amma wanda abun ya ritsa da su na cikin wani mawuyacin hali,” in ji sa.