✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abun da ke hana samun isasshen barci

Shin kun san cewa kashi 30 na ma’auratan da ke rabuwa saboda rashin barci isasshe sun fito ne daga wani yanki na kasa guda? Yayin…

Shin kun san cewa kashi 30 na ma’auratan da ke rabuwa saboda rashin barci isasshe sun fito ne daga wani yanki na kasa guda?

Yayin da barci ke matsayin hutu, ba kowa ke samun sa mai dadi kuma isasshe ba, duk kuwa muhimmanci mutane kan ba shi. Hakan ta sa a lokuta da yawa rashinsa ke haifar da matsala musamman tsakanin ma’aurata.

Ku biyo mu domin jin sanin da masana suka gano yana haifar da rashin samun isasshen barci da rabuwar ma’aurata da kuma mafita daga matsalar.

Binciken da cibiyar SleepStandard ta gudanar kan Amurkawa 1,008 masu shekaru 18 zuwa 73 ya tattaro wasu matsalolin da hada wurin kwanciya ke haddasawa a tsakanin ma’aurata:

Kwanciya tare

Kashi uku bisa hudun ‘yan kasar sun ce hada wurin kwanciya da ma’auransu na hana musu samun isasshen barci.

Kazalika bullar tun bullar annobar coronavirus kashi daya bisa hudu na wadanda aka yi wa tamboyoyi sun ce ba su nutsuwa a wurin barci sai idan su kadai kwanta.

Abin da ke hana jin dadin barci

Yawan minshari shi ne babban abin da ke hana kashi 53 na ma’aurata samun isasshen barci, kamar yadda binciken ya gano.

Wasu kan kasa yin barci saboda tsarin lokacin barcinsu ya bambanta da na ma’auransu. Shi ma yawan motsi a lokacin barci da karar na’urorin laturorin ma’aurata kan hana wasu takwarorinsu barci.

Binciken ya kuma gano cewa mata sun fi yiwuwar kaurace wa wurin kwanciyarsu idan hadawa da mazansu na takura su.

Bayan haka, ma’aurata ‘yan shekara 23 zuwa 38 sun fi yiwuwar matsowa da rungumar juna a lokacin kwanciya fiye da ‘yan shekara 55 zuwa 73. Hakan ke nuna tasirin shekaru wurin kawo tazara tsakanin ma’aurata a wurin kwanciya.

Hanyoyin samun isasshen barci

Sakamakon, haka ma’auratan kan bi hanyoyi domin inganta yanayin barcinsu.

SleepStandard ya gano kashi 59 na Amurkawa ma’auratan sun zabi daina kwanciya tare a gado guda domin samun walwala yayin barci. Wannan kuma shi ne abin da kashi 39 na ‘yan kasar.

Sabanin masu kaurace wa kwanciya tare, galibin ma’aurata da aka yi binciken da su sun zabi su kara girman gadonsu.

Kashi daya bisa hudu kuma sun zabi ci gada da kwanciya tare, amma kowa da mayafinsa.

Illolin rashin gamsashen barci

Fiye da rabin Amurkawa ma’aurata ba su fiye saduwa da juna ba idan dabi’ar barcin ma’auransu ya cutar da su. Suna kuma yawan samun sabani idan suka kwanta tare da ma’auran da ke hana su jin dadin barci.

Mata sun ninka maza saurin neman rabuwa da ma’auransu idan suka rasa kyakkyawar mu’amala a lokacin kwanciya.

Binciken ya kuma gano cewa kashi 30 na mutanen da aurensu ke mutuwa saboda matsalolin masu nasaba da rashin wadataccen barci sun fito ne daga yankin Kudancin Amurka.