✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abuja: Yadda mutane ke kwana a cikin motoci da gine-ginen da ba a kammala ba

In da muna da zabi ba za mu zabi wannan rayuwa ba.

Talauci da rashin tsaro da neman rayuwa mai dadi ne suke sa ’yan Nijeriya yin tururuwar zuwa Abuja; fadar kasar nan.

Sai dai kuma a karshe Abujar kan zame musu marmari daga nesa, inda suke haduwa da rayuwar kunci da wahalhalu.

Da dama ba su da muhallin kwanciya, inda suke samun mafaka a gidajen da ba a kammala ba ko su rika kwana a cikin motocinsu ko a tsofaffin motocin da suke yashe a garejoji kamar yadda bincike Aminiya ya gano.

Ga ’yan Nijeriya da dama da masu ziyartar Babban Birnin Tarayyar, Abuja sukan dauka wata aljannar duniya ce, mai kankararrun gine-gine da kyawawan hanyoyi da suke cike da wutar kan titi wadda aka kawata hanyoyinta da itatuwa ababen burgewa.

Sunanta ya yi tambari a mujallu da kafafen sadarwar zamani wadanda suke kwarmata kyanta tare da bayyana ta da birni mafi saurin bunkasa a Afirka.

A cikin birnin akwai dogayen ginegine da suke nuna yadda harkokin siyasar kasa suke tafiya tare da taken ‘Cibiyar Hadin Kai’ da ke nuna kasancewarta gida ga kowa.

To amma a cikin birnin sabanin haka ne ake iya gani, inda mazaunansa suke fama da wahala wajen samun wurin kwanciya don kauce wa ruwa da rana da sanyi.

Mummunar rayuwar talauci da rashin tsaro sun tilasta mutane barin garuruwansu don neman kyakkyawar rayuwa a Abuja, ba laifi ya sa suka gudo ba, a’a sun zo ne suna neman mafaka tare da zimmar dandanar zuman dukiyar da take da shi.

Daga shekarar 2020 zuwa yanzu, bayanai daga Macrotrend, wata cibiyar tara bayanai ta duniya sun ce nutane da dama daga yankunan kasar sun komo Abuja, inda birnin ya hadu da karuwar jama’a da sama da kashi 22.81.

Bayanan sun nuna mazauna Abuja sun karu daga mutum miliyan 3 da dubu 278 a shekarar 2020 zuwa miliyan 4 da dubu 26 a shekarar 2024.

Hasashen Macrotrend ya nuna cewa zuwa nan da shekarar 2035, adadin mazauna Abuja na iya kaiwa miliyan shida.

Sai dai kuncin rayuwar da ake fuskanta a birnin na karuwa, inda karuwar kudin hayar gidaje ta tilasta mutane da dama rasa muhalli; suka koma kwana a gine-ginen da ba a kammala ba ko a cikin motoci ko akurkin katako da ake kira baca a wasu sassan.

Masu kwana a ginin asibitin da aka yi watsi da shi Iska mai kadawa sosai, warin bola da karnin fitsari ne suke maraba ga duk mai shiga ginin asibitin da aka yi watsi da shi ba a kammala ba, wanda a yanzu ya zama gida ga sama da mutum 100, ciki har da yara a yankin Utako da ke birnin Abuja.

A cikin wannan gini mazaunansa suke samun ’yan wuraren da za mayar dakunan kwana son su saka kafadunsu da kuma inda za su rika girki.

Babu wurin bahaya, wannan kan sa mazaunansa su yi tattaki da dare zuwa bololi da filaye su biya bukatunsu.

A cikin wannan gini da ba a kammala ba ne wakilinmu ya iske Binta Yahuza wata mai shekara 42 da ta samu mafaka a Babban Birnin Nijeriyar, bayan ta gudo daga matsalar tsaro da ta rabo ta da gida Jihar Katsina.

Yanzu tana rayuwa ce tare da ’ya’yanta biyar da kuma wasu marayu uku.

Binta ta ce, “Ba za mu iya zama a Katsina ba, saboda rashin zaman lafiya.”

Muryarta na rawa cike da tsoro, inda ta bayyana yadda ta shafe shekara uku kafin ta samu isa ga ginin.

“A nan Abuja, mun sa ran samun zaman lafiya da damar gina rayuwa mai kyau,” in ji ta.

Amma rayuwar cike take da kunci.

Binta daya ce daga cikin ’yan Nijeriya miliyan 24.4 da Hukumar Kula da Yawan Jama’a ta Duniya ta bayyana da marasa muhalli, saboda ba su da ingantaccen gida ko damar samunsa.

Kuma bayanan sun nuna Nijeriya a matsayin kasar da ta fi marasa muhalli a duniya a shekarar 2023, abin da ke nuna mutane da dama suna zaune ne ba tare da samun abubuwan da suka zama lalura a rayuwa ba.

Marar muhalli a cewar Cibiyar Marasa Muhalli ta Duniya da Hukumar Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya, shi ne wanda yake kwana a kan titi ko fili ko a cikin mota ko muhalli na wucin-gadi ko sansanin mutanen da aka raba da muhallinsu da kuma wadanda suke zaune a gidaje ko wuraren da ba su dace ba, ko ba su da tsaro.

Yayin da Binta ta fado a cikin wannan rukunin mutane, tana sayar da awara ce domin neman abin kare bukatu, inda ’ya’yanta suke taimaka mata wajen soya doya da hada hannu don samun abin da za su rike kansu.

Sai dai dan abin da suke samu ba zai isa su kama gidan haya ba, kuma hauhawar farashin kaya ta dada jefa su a cikin kunci.

“Mukan sayi taliya a baya a kan Naira 200, sai ta koma 300 yanzu kuma Naira 800,” ta fada cikin damuwa.

A cikin dai wannan gini Aminiya ta iske Chioma Sunday, wadda wahala ta sa ta tsofe.

Kamar Binta, Chioma mai shekara 30 kuma uwar ’ya’ya hudu tana zaune a Abuja sama da shekara biyu, kuma ta ce an raba iyalanta daga gidansu na katako ne a Utako.

Ta ce bayan ta dawo daga kauyensu lokacin da ta je bikin biso sai ta iske ma’aikatan gwamnati sun rushe gidansu.

Ita da iyalinta sai suka tare a bangaren ginin asibitin da ba a kammala ba.

Duk da cewa tana sayar da alala ne, Chioma ta ce, tsadar rayuwa a Abuja babu shakka ta sa ya zama birni mafi tsada a Nijeriya, wanda hakan ya sa ta mayar da biyu daga cikin ’ya’yanta zuwa kauye a Kudu maso Gabas.

Wakilinmu ya kuma iske Asabe Umar mai shekara 54 tana zaune a kan wani dutse a dakin da ba ya da tagogi ko kofa tana girka abinci.

’Yar asalin Karamar Hukumar Mangu a Jihar Filato, Asabe ta ce ta rasa wurin zama ne bayan rasuwar mijinta.

Uwar ’ya’ya 12, ta ce nauyin ’ya’yanta ya yi mata yawa, duk da cewa uku daga cikinsu sun yi aure.

“In da muna da zabi ba za mu zabi wannan rayuwa ba,” Asabe tana fadi tana mai nuni da yanayin dakin da take ciki.

A yayin da asibitin da aka yi watsi da shi ya zamo mafaka ko muhalli ga marasa gidaje, mazaunansa sun tsara kansu zuwa rukuni-rukuni domin kauce wa rikici ko aikata barna.

Horore Damachibo, wanda ya fito daga Jihar Kuros Riba, shi ne yake aiki a matsayin shugaban tsaro kuma mai kula da wannan al’umma mai mutane sama da 100. Ya ce ginin yana shirin rushewa.

Matsayin Damachibo ya zo daidai da rokon mazauna ginin – rokon samun taimako don su sake gina rayuwarsu daga zama a ginin asibitin da ba a kammala ba.

Wasu na kwana a motoci Basiru Isah, wani direban tasi mai shekara 32, Aminiya ta iske shi zaune a kan gabar motarsa yana cin tuwon masara da miyan kubewa a kwanon roba.

“Wannan shi ne abincin dare,” ya fadi yana murmushi a daidai lokacin da yake kokarin hadiye lomar da ya kai bakinsa.

Wakilinmu ya iske Isah ne da misalin karfe 11:30 na dare, a kusa da gidan nai na Megada ke Jabi, Abuja.

Yana daya daga cikin direbobin tasi da dama a Abuja, wadanda suke kauce wa tsadar rayuwa da ta man fetur da sauran bukatun rayuwar yau da kullum.

Kuma yayin da wasu suke fakewa a gidajen da ba a kammala ba, ’yan tasi da dama kamar Isah suna mayar da motocin wuraren kwanansu.

Matsalar da ake samu a tsakanin dan kudin da suke samu don sayen mai da abinci da muhalli da kuma biyan mai mota, ta zamo abar da ke sa direbobi a tsaka-mai-wuya a kullum, direbobin da suka ce sukan ziyarci iyalansu da suke wajen Abuja ne kawai a karshen mako.

Ga wasu kuma ba su ma tunanin kama gida; sun gwammace su rika kwana a cikin motocinsu.

Idan dare ya yi sai su mayar da kujerar baya tamkar gado. Sukan dan saukar da gilashin motar don samun iska, yayin da suke rufe motar da gidan sauro.

Isah da sauran direbobi sukan yi haka idan lokacin barci ya yi. “Duk lokacin da Allah Ya sa na zo aiki, nakan koma gida ne kawai a karshen mako,” in ji Isah.

Kwana a cikin motarsa ba zabi ba ne, a’a lalura ce saboda tsadar kudin mai.

Kamar sauran masu karamin karfi da matsakaita, sun ce ba su ma maganar kama hayar gida a Abuja; inda ma suke da zabi shi ne wajen birnin a kauyukan da suke jihohi makwabta.

“Duk lokacin da zan je gida a motata, nakan sha mai akalla lita takwas, wanda yanzu ya kai Naira dubu biyar,” in ji shi.

Wannan ya dara abin da yake kashewa na Naira dubu uku a kan mai a baya, wanda ya isa ya sa ya je ya dawo a kullum har ma ya samu ragowa.

Ya ce a yanzu abin da yake kashewa ya dara abin da yake samu saboda tsadar mai inda aka barinsa da fama da yadda zai nemo cikon abin da yake kashewa balle a yi maganar kudin da zai dauki nauyin iyalinsa har ya kama hayar gida a kusa da Abuja.

Wani bayani na Babban Bankin Nijeriya (CBN) na shekarar 2019 ya ce, Nijeriya tana da karancin gidaje kimanin miliyan 17 zuwa miliyan 22.

Rahoton ya jingina abin da ke kawo haka a kan karuwar talauci, karuwar yawan jama’a da kaura zuwa birane.

Sai dai bayanai na bayan nan daga Dataphyte; wata kafar bayar da bayanai ta Nijeriya sun nuna cewa gibin gidaje a Nijeriya ya karu zuwa miliyan 23 a shekarar 2023.

Aliyu Wamako, wanda ya taba zama Shugaban Kungiyar Bunkasa Samar da Gidaje ta Nijeriya (REDAN), ya ce akasarin ’yan Nijeriya ba su iya mallakar gida, duk da cewa hare-haren ’yan ta’adda da ’yan bindiga da bala’o’i da dama kamar ambaliya suna tilasta mutane da dama yin kaura zuwa manyan birane kamar Abuja.

“Idan akwai wadatattun kudi za a samu wadatattun gidaje. Amma ba za ka iya zuwa banki ka karbi rance a kan kudin ruwa kashi 38 cikin 100 ba,” in ji shi.

Sunday Dako, dan tasi mai shekara 54 ba ya da gida kuma ya ce al’amura sun dada sukurkucewa.

Dako bai kama gidan haya ba, don haka yake kwana a cikin motarsa.

Ya ce, “Nakan kwana ne kawai a daki a gidan abokina lokacin da matarsa ba ta nan.”

Ya kara da cewa yana amfani ne da bayin kudi wajen biyan bukatunsa.

Kamar Dako, Shehu Abdullahi, direban tasi mai shekara 63 ya ce, motarsa ita ce wajen aikinsa kuma gidansa.

Abdullahi wanda ya fito daga Jihar Kano ya shafe shekara 27 yana aiki a banki har zuwa lokacin da aka sallame shi a shekarar 2016.

Ya dawo Abuja don neman abin rayuwa. Sai dai karancin aiki ya sa Abdullahi ya kama tukin tasi don neman na sawa a bakin salati.

Ya ce, “Daga farko wani abokina ya saya min mota in yi sana’ar tuki. Amma saboda yawan gyara na kasa rike ta. Dole na sayar da motar yanzu haya nake karba ina biyan mai ita Naira dubu 20 a kowane mako.”

Kamar sauran direbobi, shi ma yana fama da manyan matsaloli biyu; karuwar kudin man fetur da tsadar kudin hayar gida.

Tsadar kudin mai ta kara masa matsala kan yadda zai iya hada Naira dubu 20 din da yake biyan mai motar da kula da iyalinsa da kama gidan haya. Wannan ya sa ya fice daga gidan hayar.

“Na kama gidan haya mai kyau, amma kara kudin man fetur ya sa ba zan iya biya ba. Dole na hakura na kama daki daya ga iyalina yayin da nake kwana a cikin tasin,” in ji shi.

A cikin wurin ajiye kaya na motarsa ce Abdullahi ke ajiye suturunsa. Ba masu yawa ba ne, amma sun ishe shi ya yi mako da su.