A ranar Laraba da daddare ne aka samu labarin rasuwar tsohon jarumin masana’antar Kanywood, Sani Garba SK, sannan aka yi masa jana’iza da safiyar Alhamis.
Rasuwar marigayin wanda ya sha fama da jinya na tsawon lokaci ta girgiza masana’antar matuka.
- An haramta yin dariya na tsawon kwana 11 a Koriya ta Arewa
- An yi karin mafi karancin albashi zuwa N137,000 a Turkiyya
An sha yada jita-jitar marigayin ya rasu, kafin daga baya a gane ba haka ba ne.
A watan jiya ma an yi jita-jitar, inda ya fito ya bayyana cewa idan lokaci ya yi ba sai an yi jita-jitar ba ma zai rasu.
Daga cikin abubuwan da za a tuna marigayin akwai:
Fim din Badali
Fim din Badali tsohon fim ne da ya tashe sosai a lokacinsa.
Wakar fim din ga ‘Sai ruwa ruwa na malale’ wanda Ali Nuhu da Abida Mohammad suka fito har yanzu masoya tsofaffin wakoki na sauraronta.
A cikin fim din ne Sani SK yake cewa wani yaro “Za ka ci banana?” Da kuma inda yake cewa ‘Kar ka ba da ni mana Dumbadus’.
Wadannan kalmomi da ya yi amfani da su an dade ana kiransa da su.
Har yanzu wasu masu kallon fina-finan Kannywood na da da ‘Za ka ci banana’ suke masa lakabi.
Dabi’a
Fim din Dabi’a marigayin ya fito ne a matsayin mijin jaruma Hadiza Kabara, inda ya karo amarya sannan ya zo da niyyar ya hada su.
A nan aka yi wakar “Ya matana nasiha zan muku babba”.
A cikin wakar ce a karshe da ya nuna wa Hadiza Kabara alamar wariya da wulakancin cewa talaka ce, sai ta yi Larabci ta nuna musu cewa ilimin addini ya fi.
Barkwanci
Daga cikin jaruman Kannywood, Marigayi Sani SK, zai dade ba a manta shi ba, musamman yadda yake kawo barkwanci cikin fina-finan da ba na barkwanci ba.
Ko a alhaji ya fito a fim, yakan yi amfani da kwarewarsa wajen jefa barkwanci a ciki domin nishadantar da masu kallo.
Dadewa ana yi
Marigayi Sani SK ya dade ana damawa da shi a masana’antar Kannywood, inda yawancin tsararrakinsa fim din ya daina yi da su.
Ko a kwanan nan ya fito a fim din Ali Nuhu mai dogon zango na Gargada, inda ya fito a matsayin mijin Sarah (Diamond Zahra) inda suka hada wa Lawan Ahmad tarko domin su damfare shi.
Ko a lokacin da ake daukar fim din ba shi da lafiya domin yawancin lokaci a zaune yake, sannan jikinsa babu karsashi.