A jawabin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi lokacin rantsuwar karbar mulki ranar 29 ga watan Mayu ya bayyana cire tallafin man fetur, abin da ya haifar da karin kudin man nan take daga Naira 195 zuwa 540 kowace lita daya.
Masu goyon bayan cire tallafin sun bayyana yadda za a iya sarrafa kudaden tallafin wajen bunkasa bangarorin ilimi da kiwon lafiya da noma da gyara hanyoyi da kyautata sufuri da sauran fannoni a kasar nan.
- Za mu tabbatar da tsaron masu yi wa kasa hidima a Yobe — Buni
- Abubuwan da suka kamata a sani kan cutar Diphtheria da take yaduwa a Najeriya
Sun ce Najeriya ta kashe fiye da Naira tiriliyan hudu wajen ba da tallafin man fetur a bara.
Aminiya ta ruwaito yadda cire tellafin ya haifar da tashin gwauron zabon farashin kayayyaki inda ya fi muni a bangaren kayan abinci da harkokin sufuri.
Sai dai zuwa yanzu bayan wata daya da cire tallafin babu wani abin da gwamnatin ta yi wa ’yan kasa don rage musu radadin da suka shiga a sanadiyyar cire tallafin man.
A jawabin Shugaba Tinubu ga ’yan Najeriya a Ranar Dimokradiyya, Shugaban ya ce dole ’yan kasa su yi hakuri tare da jure daukar wannan mataki domin ceto kasar daga komawa baya.
Shugaba Tinubu ya ce yana sane da irin halin kuncin da ’yan kasa za su fada a sanadiyyar cire tallafin, sai dai ya ce hakan zai ’yantar da tattalin arzikin kasa da wasu ’yan tsiraru kawai ke amfana da shi.
“Gwamnatin da zan jagoranta za ta mayar wa ’yan kasa kudaden ta hanyar zuba jari a fannonin gine-gine da ilimi da kiwon lafiya tare da bunkasa sauran fannoni,” in ji shi.
Kafin cire tallafin Aminiya ta ruwaito yadda Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC), Mele Kyari a ranar 17 ga watan Fabrairun 2023 yana cewa Najeriya na kashe sama da Naira biliyan 400 a kowane wata a kan tallafin man fetur.
Ya bayyana haka ne a Abuja yayin bikin da NNPC ya yi da kuma samar da NNPCL.
“A yau, bisa ga tanadin doka, akwai tallafi wajen rarraba man fetur a cikin kasa.
“A ka’idar da ke akwai a yanzu, Naira 315 ne ake sauke kowace lita ta mai.
“Ga abokan cinikinmu nan kowane muna ba shi lita daya a kan Naira 113. Hakan na nufin akwai bambancin kusan Naira 202 kan kowace lita da muke shigo da ita kasar nan.
“Idan ka ribanya Naira 202 sau lita miliyan 66.5 ka sake ribanya shi na kwana talatin zai ba ka Naira biliyan 400 a kowane wata,” in ji shi.
Abin da za a iya yi da kudin wata daya na tallafin fetur da aka cire
Nazarin Aminiya ya gano da Naira biliyan 400 da aka kubutar daga ba da tallafin a wata daya za a iya gina bohul-bohul 400,000 a sayo safa bas-bas 20,000 ko a gina asibitocin karkara 13,000.
Kuma adadin zai iya gina akalla hanya mai tsawon kilomita 200 ko sayo taransifomomi 40,000.
Duk da yawancin ayyukan gwamnati ana ba ’yan kwangila ne, lissafin da wakilinmu ya yi bai hada da yadda za a ba ’yan kwangila ba, ya yi ne kan yadda farashi yake a kasuwa wanda kowa zai iya samarwa cikin kankanen lokaci matukar yana da kudi.
Samar da asibitoci 13,000
Binciken Aminiya ya gano Najeriya tana da nau’o’in cibiyoyin kiwon lafiya biyar ne kamar yadda Hukumar Kula da Kiwon Lafiya daga Tushe ta Kasa (NPHCDA) ta bayyana.
Kashi na farko, kamar yadda hukumar ta bayyana shi ne ya kamata ya rika kula da kauyen da ke da mutum 500.
Na biyu wanda zai iya kula da lafiyar mutum 2000 zuwa 5000, yayin da na uku kuma Cibiyar Kula da Lafiya a Matakin Farko (PHC) wadda kowace karamar hukuma cikin 774 ke da shi wanda mafi karanci su ne masu gunduma 10.
Kashi na hudu manyan asibitoci wadanda gwamnatocin jihohi ke kula da su wadanda ake samu ran samun kowane daya a dukkan kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar nan.
Kashi na karshe kuma su ne Asibitocin Koyarwa (Teaching Hospitals) wadanda su kuma suke wuyan Gwamnatin Tarayya kuma ake samun su a dukkan jihohi 36 da ke kasar nan.
Wuraren kiwon lafiya a matakin farko nan ne ake sa ran samun kula daga ma’aikata a cikin al’umma.
Duk wuraren da za su zama waje na farko da za a tuntuba don neman lafiya sun zama wajen kula da lafiya a matakin farko.
Yawancin mutane kan ziyarci karamin likita ne idan ba bukata ce ta gaggawa ba domin duba lafiyarsu a matakin farko kamar likitan hakori da sauransu.
Yawancin irin wadannan wurare ana samun su ne a kananan garuruwa ko karkara kuma ma’aikatansu kan yi aiki a cibiyoyin kiwon lafiya ko kananan asibitoci.
Yawancin irin wadannan wurare sukan mayar da hankali ne wajen duba marasa lafiya da bayar da magungunan cututtukan da aka fi samu a yankunan gwargadon kwarewarsu.
Daga nan ne za su bayar da shawara tare da tura su zuwa manyan asibitoci ko asibitocin koyarwa inda marar lafiya zai samu cikakkiyar kulawar da ta dace.
Hakazalika za su iya tura mutum wajen wani kwararren da ya dace.
Duk da cewa cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ne hanya ta farko don cim ma kudirin Muradun Karni na Majalisar Dinkin Duniya mai dorewa kan harkar lafiya, a Najeriya yawancin mutanen karkara ba su cika zuwa wadannan wurare ba saboda rashin kyansu, hakan ne ma ya sa Shugaban Hukumar NPHCDA, Dokta Faisal Shu’aibu ya ce har yanzu cibiyoyin samar da lafiya a matakin farko suna nan a mataki na rashin ci gaba.
Matsakaicin irin wannan asibitin a Najeriya shi ne wanda yake da gado 15 zuwa 20 na marasa lafiya yayinda wasu ma wurin ajiye gado hudu kawai suke da shi kamar yadda rahoton bin diddigi ya nuna.
Aminiya ta fahimci hakkin samar da cibiyoin lafiya kashi na 1 da na 2 da na 3 yana wuyar Hukumar NPHCDA ne.
Kasafi da hukumar ta nuna na abin da take samar da kashi a farko na irin wadannan asibitocin shi ne Naira miliyan 21.
Shi kuma kashi na biyu hukumar ta bayyana zai lashe kusan Naira miliyan 22 yayin da kashi na uku zai lakume Naira miliyan 30 kowane daya.
Aminiya ta gano cewa bisa kiyasin Naira miliyan 30 wajen samar da cibiyar lafiya a matakin farko (PHC), Gwamnatin Tarayya za ta iya gina guda 13, 000 a jihohi 36 da muke da su daga Naira biliyan 400 na tallafin fetur da cire na wata daya kawai.
Bohul-bohul 400,000 a karkara
Kwararru sun ce abin da ake kashewa wajen haka bohul don samar da ruwa ya danganta ne da zurfi da kuma kayan aikin da ake bukata yayin haka bohul din.
Binciken da Aminiya ta yi ta gano haka kowane bohul daya a kauyuka ko unguwanni masu mutum 500 zai ci Naira 80,000 ne zuwa Naira miliyan daya.
Idan aka dauki Naira miliyan daya, Gwamnatin Tarayya za ta iya haka bohul 400,000 a kananan hukumomi 774 da kudin da ta samu na tallafin da ta cire Naira biliyan 400.
Hakan na nufin kowace karamar hukuma za ta samu akalla bohul guda 516 idan ta haka guda 400,000 a kananan hukumomi 774.
Samar da taransfomomi 26,000
Najeriya na samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 5000 ga mutanenta miliyan 200.
Duk da cewa Najeriya ce giwar Afirka a yawa da karfin tattalin arziki amma ita ce mafi koma-baya a duniya a fannin samar da wutar lantarki.
Duk da yake gwamnati ta ce tana da halin da za ta iya samar da megawatt 10,000 amma sai ga shi ta buge a megawatt 5,000 kacal.
Hakan ya nuna akalla mutum miliyan 85 na ’yan Najeriya ba su iya samun wutar lantarki, kamar yadda Bankin Duniya ya bayyana.
Bankin ya ce Najeriya tana asarar Naira tiriliyan 22.4 kowace shekara saboda karancin wutar lantarki.
Kanana da matsakaitan harkokin hakasuwanci da sana’o’i suna taimaka wa kusan rabin abubuwan da kasar take samarwa sun gamu da mummunar koma-baya saboda rashin wadatacciyar wutar lantarki da gaza samar da taransifomomin a unguwanni da kauyuka.
Hukumar REA ce ke da hakkin samar da wutar lantarki a yankunan karkarar Najeriya.
Kuma binciken Aminiya ya nuna ana samun madaidaiciyar na’urar taransifoma mai ba da wutar lantarki mai karfin 25KBA a kan Naira miliyan 10 yayin da mai karfin 35KVA ake samunsa a Naira miliyan 15, duk da an dan samu kari kadan sakamakon faduwar darajar Naira inda Dala ya tashi daga Naira 461 zuwa 730 kuma na’urorin samar da wutar lantarkin ana shigowa da su daga kasashen waje.
A lissafin na Naira miliyan daya, Gwamnatin Tarayya za ta iya sayo taransfomi da ba su gaza 26,000.
Bayanan Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) sun nuna adadin mazabun kansila da ake da su a Najeriya guda 8,809 ne.
Da wannan adadi kowace mazaba za ta samu na’urar taransfoma guda uku.
Samar da manyan motoci don rage tsadar sufuri Tsarin harkokin sufuri a manyan motoci na daga cikin tsare-tsare mafiya inganci da kasashe da dama a duniya ke amfani da shi don saukaka wa al’ummarsu wajen zirga-zirga a cikin gida.
Amma a Najeriya tsarin na fuskantar tasgaro saboda dabi’ar rashin kula da gyare-gyare.
Mafi yawan jihohi a yau ba su da manyan motocin zirga-zirga mallakinsu idan ka cire wanda Gwamnan Jihar Barno, Babagana Zulum ya sayo guda 80 don saukaka harkokin sufuri da zirgazirga ga mutanen jiharsa saboda rage radadin cire tallafin man fetur.
Tsakanin shekarar 2003 zuwa 2007 Gwamnatin Tarayya ta samu isassun motocin sufuri a Abuja lokacin da tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i yake Ministan Abuja wanda sannu a hankali suka yi ta raguwa har zuwa yau din nan da za a neme su a rasa.
A irin halin da ake ciki na tsanani sakamakon cire tallafin man fetur da hauhawar farashin sufuri ya zama dole ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi su yi koyi da Gwamna Zulum wajen samar da motocin zirga-zirga.
Aminiya ta bincika daga dillalan motoci inda ta samu labarin farashin mota safa (Coaster) da ke daukar akalla mutum 30 kudinta yana kamawa daga Naira miliyan 18 ne zuwa miliyan 20, ya danganta.
Idan aka dauki na Naira miliyan 20 gwamnati za ta iya sayo safasafa 20,000 da wannan kudi na tallafin man fetur Naira biliyan 400 da ta cire a wata daya kacal.
Hakan na nufin kowace karamar hukuma za ta samu safa 25 na motocin Kosta.
Ba da bashi marar ruwa na Naira miliyan 10 ga kananan ’yan kasuwa miliyan 39
Kididdigar Hukumar Kula da Kanana da Matsakaitan Kasuwanci (SMEDAN), ta nuna Najeriya na da kanana da matsakaitan ’yan kasuwa miliyan 39.
A kididdigar da SMEDAN ta gudanar a shekarar 2020 aka kuma fitar a 2021 da hadin gwiwa da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce lamarin ya sauko ne daga miliyan 41.
SMEDAN ta alakanta raguwar da barkewar cutar COVID-19 da kuma wasu matsaloli da suka dabaibaye harkar kanana da matsakaitan kasuwanci wajen farawa ko kuma dorewar kasuwar.
Ke nan da wannan adadi na miliyan 39 kowane matsakaicin dan kasuwa zai iya samun Naira miliyan 10 na kudin da babu ruwa a ciki mafi karanci domin bunkasa ayyukansa daga cikin kudin tallafin mai na wata daya kacal.
Harkokin tattalin arziki za su ruguje idan ba a samar da tallafi yanzu ba
Kungiyar Tabbatar da Amana Wani kwararre kuma Daraktar Cibiyar Tabbatar da Gaskiya da Amana a Harkokin Kudi (Centre for Fiscal Transparency and Integrity Watch – CefTIW), Umar Yakubu, ya ce Gwamnatin Tarayya ta cire tallafi a wasu abubuwa da suka hada da kananzir da man dizal inda a nan ma ta samu rarar tiriliyoyin Naira.
Sai dai ya ce cire tallafin man fetur na bukatar daukin gaggawa don tallafa wa ’yan Najeriya ko kuma harkokin tattalin arzikin kasar nan ya kama rugujewa sakamakon wannan tsari.
“Illar da za a fara samu ita ce hauhawar farashi daga kashi 22.2 a watan Afrilun 2023.
“Farashin kayan masarufi ya tashi zuwa kashi 24.7 a Afrilun 2023, daga kashi 18.37 a watan Afrilun 2022.
“Kamar yadda Bankin Duniya ya bayyana, kusan ’yan Najeriya miliyan 10 aka kiyasta za su bi sake talaucewa ya zama masu fama da talauci su kai mutum miliyan 130.
“Wato karin wasu miliyan 10 da ba su kai matakin zama kananan ko matsakaitan ’yan kasuwa ba wanda wannan tsarin zai haifar.
“Kowace masana’anta akwai iya adadin wadanda za su iya dauka don haka akwai bukatar kawo dauki na gaggawa,” in ji shi.
Ya yi kiran a yi gaskiya wajen gudanar da rabon tallafin. “Amma a daya hannun, wadanne matakai aka dauka don tsarewa tare da sarrafa tiriliyoyin nairorin da aka samu wajen ganin an yi gaskiya da adalci?
“Sun ce za su sanya a asibitoci da makarantu, ko sun canza ne?
Rahotanni sun nuna kashi 70 na almundahana na faruwa ne wuraren gwamnati ta irin wannan hanya don haka dole a bayyana yadda za a bi don amfanin ’yan kasa,” inji shi.